Yadda sufeto janar na Najeriya ya nemi dakatar da El-Rufai ziyartar Sanusi a Awe

0

Majiya mai tushe ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa sufeto janar na’yan sandan Najeriya Muhammed Adamu ya gargadi gwamna Kaduna Nasir El-Rufai kada ya kuskura ya ziyarci Sanusi a garin Awe ranar Alhamis.

Majiyar ya tabbatar mana cewa Sufeto Adamu ya shaida wa El-Rufai cewa zayarar sa zai iya tada zaune tsaye kuma idan har ya dage sai ya tafi ranar Alhamis din, ‘Yan sanda za su dakatar da shi.

Daga baya sai ya sanar wa gwamnan jihar Nasarawa da ‘Yan sandan jihar inda suka yi na’am da wannan himma na sa. Sai dai kash, El-Rufai bai samu daman yin wannan tafiya ba saboda taron da ya halarta a fadar shugaban kasa da ya kaisu yamma.

A ranar juma’a da ya kama hanya sai kuma faduwa ta zo daidai da zama, kotu ta tsinka kacar da aka nannade Sanusi da shi. Zai iya watayawa yadda ya ke so.

Sai dai kuma kakakin rundunar ‘Yansandan Najeriya, Frank Mba ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ba shi da damar cewa komai game da wannan abu.

” Tsakanin gwamna El-Rufai da sufeto Janar akwai kusanci mai kyaun gaske.Za su iya tattaunawarsu baki alaikum ba sai na sani ba. Saboda haka bani da ta cewa a yanzu.

Tuni dai El-Rufai da amininsa tsohon sarkin Kano Sanusi suka dare jirgi zuwa Ikko tare da iyalan sarki Sanusi.

Share.

game da Author