Yadda na rika kama mijina na lalata da matan mamun sa ga shi Limamin Masallaci – Mata

0

Uwargidan wani Limamin masallaci a jihar Legas Rebecca Yusuf ta shigar da kara kotu a garin Legas tana rokon kotu ta raba aurenta da mijinta mai suna Yusuf da ta kama sau dayawa yana lalata da matan mamumsa sa.

Matar tasa mai suna Rebecca ta bayyana cewa mijin ta Yusuf ba mutumin kirki bane domin yakan zagaya ya rudi matan mamun sa yana lalata da su.

Ya’yan Rebecca da Yusuf guda hudu ne kuma sun shekara 15 a aure.

Ta ce wata rana ta kama mijinta Yusuf yana lalata da matar wani mutumi dake sallah a masallacin da ya ke limanci.

“ Ina ganin su sai na yaga wa matar kayan dake jikinta sannan na saka ihu. Yusuf ya roke ni da na daina ihu domin kada mutane su ji mijin wannan mata ya sake ta.

Rebecca ta ce wannan ba shine karon farko ba da Yusuf ke lalata da matan mamun sa . Ba masu aure ba ma har da ya’yan su wadanda basu yi aure ba.

Bayan an gano cewa Yusuf fasiki ne sai mutane da dama suka daina zuwa masallacin da yake limanci sannan kuma tana zargin cewa ko aurenta da yayi ma asiri yayi mata.

Ta ce ta ci gaba da zaman auren ne saboda ‘ya’yan su.

Yusuf ya amsa laifin sa sai dai ya ce tsautsayi ne da kuma bin Khudubar shaidan. Amma kuma ya ce ita ma matar sa tana bin bokaye, don kusan kullum sai ta dawo gida da wani kullin magani, na tsubbace-tsubbacenta kuma mazinaciya ce.

Alkalin kotun Adeniyi Koledoye ya dage shari’an zuwa 20 ga watan Maris, 2020.

Share.

game da Author