Rundunar Sojin Najeriya ta koka kan yadda mazauna Kauyukan yobe suka yi sanadiyyar Kashe dakarun Najeriya har 47 a harin kwantan bauna da suka kai musu a Alagrano, jihar Yobe.
Da yake tabbatar da wannan hari da aka kai wa sojojin Najeriya, darektan yada labarai, John Enenche ya ce, mazauna kauyukan wadannan yankuna ne suka rada wa Boko Haram cewa Sojojin za su wuce ta wannan hanya.
Enenche ya ce sojojin za so koma garin Alagro ne bayan atisayi da suka yi a yankin.
” Mazauna kauyukan ne suka rada wa Boko Haram cewa sojojin na raka makamai da mai zuwa garin Alagro, inda aka far musu.
Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES ta ruwaito yadda mahara suka kashe akalla sojoji 50 a yobe.
Majiya daga cikin sojoji ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa Boko Haram din sun kashe kusan ilahirin rundunar sojan atilare guda daya sukutum, a wannan hari da suka kai.
Sojojin na kan aikin sintiri na musamman ne kan hanyar su ta dumfarar Alargamo, sai Boko Haram suka tare su a ranar Lahadi.
An yi ta ba-ta-kashi, inda sojojin suka kori Boko Haram. Washegari Litinin kuma suka sake nausawa gaba, da niyyar karaaawa Alargamo. Boko Haram sun yi musu kwanton-bauna inda suka bude musu wuta da manyan bindigogin da ake harba gurneti da su, wato RPGs.
Majiya ta tabbatar cewa cikin sojojin da aka kashe, akwai masu mukamin manjo biyu, Flight Laftanar na Sojan Sama daya.
Sojojin na kan sintirin Operation Tamonuma ne a lokacin da aka bude musu wuta. An kuma lalata motocin da suke ciki.