Yadda cutar coronavirus ta tarwatsa wasannin kwallon kafa a duniya

0

Cutar coronavirus ta tilasta wa mahukunta a harkar wasannin kwallon kafa a duniya, dage wasannin zuwa wani lokaci.

A kasar Britaniya da nan ne ake buga wasan Premier League, an dakatar da buga wasannin saboda annobar coronavirus.

Babban dalilin kuwa shine ganin yadda wasu ‘yan Wasa suka kamu da cutar da ya sa a makonnin baya Dole aka dage buga Wasa da wasu kungiyoyin kwallon kafan kasar.

Kociyan kungiyar Arsenal Arteta, ya kamu da cutar da hakan yasa dole aka killace ‘yan wasan wannan kungiyar Arsenal.

Dyabala, na kungiyar Juventus a kasar Italiya Shima ya kamu da wani mai buga wa kungiyar baya.

A kasar Spain, an killace duka ‘yan wasan Real Madrid, na kwanaki 14 domin a tabbatar basu kamu da cutar ba.

A can Spain din an dakatar da buga kwallon kafa a kasar.

Hakan kuma gasar zakarun kwallon kafa ta nahiyar Turai, wato Chanpions League.

A halin da ake cike yanzu an dakatar duk wasannin kwallon kafa a duniya.

Masu nazari sun bayyana cewa za a samu marsala Matuka musamman a kudaden shiga da ake samu a dalilin dakatar da wasan.

” Ba a kasar Turai ba kawai hatta a Amurka da Afrika, annoban ya sa am dakatar da karkokin hadahadar kasuwanci da saka jari a harkar wasannin.

Hatta masu gidajen kwallon kafa a Najeriya sun koka kan yadda wasannin ya zai kawo musu ci baya akan hakan.

Share.

game da Author