Wata bakuwar cuta ka kashe shanu 200 a Jigawa

0

Wata bakuwar cutar dabbobi da ba a gane irin ta ba, ta kashe shanun makiyaya kimanin 200 a cikin rugagen Fulanin yankin Margadu da ke karkashin Karamar Hukumar Guri, Jihar Jigawa.

Jami’in Yada Labaran Karamar Hukumar Gurin, Sanusi Doro ya ruwaito Babban Jami’in Harkar Noma na Guri, Kabiru Haruna ya tabbatar da bullar cutar da kuma kisan da ta yi wa shanun masu yawa.

Haruna ya ce tun cikin makon da ya gabata a farkon lokacin da cutar ta fara barna aka sanar.

“Wannan annobar ciwon shanu na da alaka da shigowar wasu bakin shanu masu yawan gaske daga Jamhuriyar Nijar. Saboda yankin da Fulanin suke ya yi iyaka da Karamar Hukumar Machina ta Jihar Yobe. Ita kuma Machina ta yi iyaka da Jamhuriyar Nijar.”

Doro ya ce akasarin shanun da cutar ta kashe duk masu su ba su bari an yi musu allurar riga-kafi ba.

Sai dai kuma wani da ba ya so a ambaci sunan sa, ya ce an kai wata daya da suka sanar da jami’an karamar hukumar, amma suka ki daukar abin da muhimmanci.

“Farko da muka sanar, muka ga ba su dauki abin da muhimmanci ba, mun rika yanka wadanda suka kamu, mu na sayar wa mahauta. Sai yanzu da abin ya kusa karar mana da dabbobi masu yawan, shi ne jami’an gwamnati ke ta kame-kame.

A na sa bangaren, Shugaban Karamar Hukumar Guri, Barkono Jaji-Ajiyani, ya sa hannun amincewa a debi naira 600,000 domin a gaggauta sayo alluran da za a yi wa shanu, domin shawo kan annobar, wadda ke kashe shanu farad-daya.

Share.

game da Author