Wanda ya afka wa Buhari, ya ne mi ya rungume shi ne – Fadar Shugaban Kasa

0

Fadar Shugaban Kasa ta karyata bayanan da ake jingina wa bidiyon da ake ta yadawa dake nuna wani mutum ya afka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a wajen taro.

Femi Adeshina da ya fitar da wannan takarda ya ce wannan makircin masharranta ne kawai da makiya don su tozarta Shugaba Buhari.

” Ina so in sanar cewa wannan mutum ya nemi ya garzayo don ya rungumi shugaba Buhari ne ba wani abu ba, amma aka canja abin, ana ta yadawa wai ya afkawa Buhari don ya tozarta shi ne.

Buhari ya zazzagaya ya duba ayyuka, kums ya leka wajen bude bukin kamun kifi na Argungu. Sannan ya dawo wajen kaddamar da dalar shinkafa. A nan ne daidai an tsaya za a dauki hoto sai mutumin ya afko wa jerin gwamnoni.

Adesina ya ce ba wai wannan mutum ya afko don wani abu da ba haka ba ne kuma irin haka na faruwa a kasashen da suka fi Najeriya ci gaba.

BIDIYO: Yadda wani ya afka wa Buhari a Kebbi

Karanta nan: https://bit.ly/2Q7jfsk

Share.

game da Author