Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Muhammad Adamu, ya bayyana cewa daga ranar Litinin din nan, ya umarci dukkan ofisoshin ‘yan sanda cewa kada a rika yawan kulle mutane barkatai, saboda gudun kamuwa da Coronavirus.
Cikin wata takardar da Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda na Kasa, Frank Mba ya sa wa hannu a madadin Adamu, ya ce daga yanzu duk wanda za a kulle sai an tantance tukunna.
“Na bada umarni kada a sake kama masu kananan laifukan da ba su taka-kara sun karya ba, ana kulle su.
“Daga yanzu saboda gudun Coronavirus, kada a kulle kowa ofishin ‘yan sanda sai dan ta’adda, dan bindiga, dan fashi da makami da kuma wanda ya yi kisa. Sai kuma mai laifin da doka ta hana a bayar da belin sa kadai.”
Adamu ya kara da cewa an kulle dukkan makarantun horas da ‘yan sanda da sauran cibiyoyi, tun bayan da gwamnatin tarayya ta bada sanarwar rufe makarantu.
Daga nan ya sha alwashin cewa jami’an ‘yan sanda za su fara tilasta duk wuraren da gwamnati ta hana budewa su bi doka.
Wannan sanarwa ta nuna irin fargabar da ake yi dangane da cutar Coronavirus a suniya, ko kuma a nan Najeriya.
Ranar Lahadi ne tsohon mataimakin Shugaban Kada, Atiku Abubakar ya bada sanarwar cewa an killace dan sa domin an yi masa gwaji, kuma an tabbatar da cewa ya kamu da cutar Coronavirus.
Atiku bai dai fadi sunan dan na sa ba. Kuma bai fadi ko daga wace kasa dan na sa ya kamu da cutar ba.