Bayan ya tsige sarki Sanusi daga kujerar sarautar Kano da gwamna Abdullahi Ganduje ya yi ranar Litini, sannan kuma aka kora kasar Nasarawa, zai garzaya kotu domin kalubalantar tsigeshi da gwamnati tayi.
Lauyan tsohon sarki Sanusi, Abubakar Mahmoud, ya bayyana cewa sun garzaya Kotu ne domin kwato wa tsohon sarki hakkin sa, na yancin da dokar kasa ta bashi.
Mahmoud ya ce ba zai yiwu a tsige shi ba sannan a kore shi a hana shi walwala kamar yadda dokar kasa ta ba shi.
A ranar Litinin Gwamnatin jihar Kano ta tsige sarkin Kano Muhammadu Sanusi da kujerar sarautar Kano.
Sakataren gwamnatin jihar Usman Alhaji ya sanar da tsige Sarkin Sanusi a jawabin da yayi bayan kammala zaman majalisar zartaswar jihar ranar Litinin.
Alhaji ya ce majajalisar ta amince da tsige sarki Sanusi daga kujerar sarautar masarautar Kano daga yau Litini.
Idan ba a manta tun bayan zaben 2019 zaman aminci ya kare a tsakanin gwamnan jihar Kano da Abdullahi Ganduje da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
Gwamnan Kano Ganduje ya zargi Sarki Sanusi da kin mara masa baya a lokacin zaben sa karo na biyu a 2019.
Rantsar da shi keda wuya sai ya fara da kirkiro sabbin masarautu a jihar da ke daidai da masarautar Kano. Dama kuma Jihar Kano ita ce jiha daya tilo a Arewacin Najeriya dake Sarki mai cikakken iko daya.
Ganduje ya kirkiro sabbin Masarautu har hudu.
Masarautun sune, Rano, Gaya, Bichi da Karaye.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Muhammad Garba, ne ya sanar da haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai a wancan lokaci in ya ce hakan ya biyo bayan rusa masarautun ne da kotu tayi a bisa dalilin cewa ba a kirkiro su bisa ka’ida ba.
” Ina so ku sani cewa, wasu masarautun da aka kirkkiro sun fi masarautar Kano asali da dadadden tarihi. Sun kafu tun kafin masarautar Kano. Wannan yana daga cikin dalilan da ya sa muke so mu dawo wa wadannan masarautu ikon su da martaba.
” An taba kokarin kirkiro irin wadannan masarautu amma ba su dore ba, a yanzu gwamnatin Ganduje na so ta ga hakan ya tabbata sannan sun tsayu gidigam.
Garba ya ce bayan haka anyi gyara ga dokar d masarautun Kano domin kawo ci gaba a jihar ne sannan ya yi kira ga majalisar dokokin jihar da su gaggauta kammala aiki a kai domin ba gwamnati damar kirkiro wadannan masarautu.
Masarautun da majalisa ta amince da su sun hada da Masarautar Rano, Gaya, Bichi da Karaye.
Discussion about this post