Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babu hannun sa a tsige sarkin Kano Muhammadu Sanusi da gwamnan Kano Abdullahi Ganduje yayi ranar Litini.
Bayan haka ya jinjina wa mutanen jihar Kano bisa kwantar da hankalin su da suka yi bayan tsige sarki Sanusi da gwamnatin jihar tayi basu ta da husuma ba.
Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa tabbas shugaba Buhari na da hannu dumu-dumu a tsige tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
Kwankwaso ya fadi haka a hira da yayi BBC HAUSA ranar Laraba.
Sanata Kwankwaso ya ce ” Jami’an gwamnatin Kano sun rika fitowa suna cewa umarni daga sama ne ya tilasta musu su tsige Sarki Sanusi.
Ya kara da cewa ba kamar yadda makusantan Buhari ke fadi cewa wai babu hannun Buhari a wannan badakala, ” Mu a jihar Kano mun san ba haka bane. Mun san cewa Buhari na sa baki a inda yake so ya saka baki a harkokin jihar Kano. ” Idan ma haka ne a nan ne ya kamata ya saka baki ba a inda ya kamata ya nade hannu ya zama dan kallo ba.”
” Tsige sarki Sanusi abin bakin cike ne garemu da duk mai kishin jihar Kano saboda Sarki Sanusi sananne ne, jarumi kuma kwararre ba a Najeriya ba, a duniya baki daya.
” Bubu gwamnati da ta san ciwon kanta ta tsige irin Sanusi a Sarauta a jihar ta.
Bayan haka Kwankwaso ya karyata rade-radin da ake yadawa wai ya taba rubutawa Sarki Sanusi takardar tuhuma a lokacin da yake gwamna a Kano.
” Ban taba rubuta masa takardar tuhuma ba. Sannan kuma babu ruwan magoya baya na wato kungiyar Kwankwasiyya a ruruta wuat rikicin Sanusi da gwamnatin Ganduje.
” Abin da ake cewa wai shine laifin Sarki Sanusi shine wai don ya ce duk wanda ya yi nasara a zaben gwamnan Kano a 2019 a bashi. Shine kwai zunubin sa. ‘Kai kaji’!.
Kuma abinda aka yi wa Sanusi, abin kunya ne kuma zubar wa mutanen jihar Kano mutunci ne a idanun duniya.
Idan ba a manta ba Gwamna Abdullahi Ganduje ya tsige Sarkin Kano Sanusi daga sarautar Kano sannan ya kora shi lardin Nasarawa.
Garba Shehu ya karyata wannan zargi inda ya ce babu ruwan shugaba Buhari a badakalar Ganduje da Sarki Sanusi.
” Buhari ba zai saka baki ba a harkar da ba hurumin sa bane. Doka bata bashi daman saka baki a wannan badakalar ba saboda haka mau cewa ya na sane kuma yana da hannu a harkar, duk soki burutsu ne, ba gaskiya a ciki.