Tir da malaman da ke kawo rudani kan coronavirus – Kungiyar Jama’atu

0

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam karkashin shugabancin sarkin Musulmi yayi tir da malaman da suke kawo rudani kan annobar coronavirus da ya mamaye duniya.

Sakataren kungiyar, Khalid Aliyu da ya fitar da sakon kungiyar ya bayyana cewa ya zama dole a wayar wa mutane musamman musulmai kai game da wannan cuta da baudaddun malaman da suke karyata cutar da matakan da gwamnati ta dauka domin a dakile yaduwar cutar.

Sanarwar ta bayyana hujjuji da dama dake nuna wajibcin musulmi ya bi uamrnin kwararru da gwamnati akan matakan da aka gindaya domin kare al’umma.

A cikin sanarwan an bayyana yadda tun a zamanin sahabban annabi ake fadwa cikin juyayi da fargaban barkewar annoba.

Da irin rasa sahaban annabi da aka yi a dalilin barkewar annoba.

An gargadi malamai su ji tsoron Allah su rika fadi wa mabiyan su gaskiya da kwantar musu da hankali da bin dokokin gwamnati domin kiyaye daga fadawa cikin tashin hankalin wannan annoba ta coronavirus tsundum.

Wasu Malamai sun rika fitowa suna sukan umarnin gwamnati na kada a fito masallatai domin kada a yada cutar. Hatta sallar Juma’a duka an dakatar. Hakan ya sa wasu su yi fatali da umarnin sun gudanar da salloli.

A jihar Kaduna an danke wasu limamai guda biyu da suka yi sallar Juma’a duk da cewa jihar ta sanar da kada ayi.

Share.

game da Author