TARIN FUKA: Dole sai an maida hankali akan yadda cutar ke ci gaba da yaduwa

0

Gidauniyar ‘KNCV Challenge TB project’ ta gudanar da bincike game da yadda yaduwar cutar tarin fuka a Najeriya ya ke dada karuwa sannan kuma kungiyar ta gano wasu wurare 70 da cutar ke ta yaduwa ba tare da gwamnati ta san da haka ba.

Gidauniyar ta gano wadannan wurare ne a yankunan Kudu maso Yamma, Kudu maso Gabas da Arewa maso Gabas.

Sakamakon binciken ya nuna cewa mafi yawan wadannan wurare na yankin karkara ne inda daga cikin mutane 1000 za a iya samun mutane dayawa dake dauke da tarin fuka.

Gidauniyar ta gudanar da wannan bincike na tsawon shekaru biyar a jihohi 14 na kasar nan.

SAKAMAKON BINCIKE

Najeriya na daya daga cikin kasashe 30 da wannan cuta ta yi wa katutu a duniya kuma itace kasa ta farko da cutar ta fi yawa a Nahiyar Afrika.

A 2019 kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta lissafo kasashe takwas da suka fi fama da cutar a duniya.

Wadannan kasashe sun hada da India, Chana, Indonesia, Philippines, Pakistan, Najeriya, Bangladesh da Africa ta Kudu inda daga ciki India, Chana da Najeriya ne kasashen da suka fi yawan mutanen dake fama da cutar.

Sakamakon binciken da UN ta gudanar ya nuna cewa a duk shekara mutane 245,000 na rasa rayukansu a dalilin kamuwa da cutar a Najeriya.

Binciken ya kuma nuna cewa a shekara 590,000 na kamuwa da cutar inda 14,000 daga ciki masu fama da cutar Kanjamau.

Shugaban gidauniyar a Najeriya Bethrand Odume ya ce tafiyar wahainiyar da gwamnati ke yi wajen hana yaduwar tarin fuka na yin barazana ga kiwon lafiyar mutane a kasar nan domin mutum daya dake dauke da cutar na iya harban mutane 15 a cikin dan kan-kanin lokaci.

Odume ya ce duk da cewa gwamnati na samun tallafi daga kungiyoyin bada tallafi dole sai ta bada nata gudunmawar domin samun nasaran yaki da cutar kwata-kwata.

Ya yi kira ga gwamnati da ta ware isassun kudade domin gano duk mutanen dake fama da cutar sannan da samar da isassun magunguna domin warkar da su.

Gidauniyar KNCV Challenge TB project na aiki a karkashin inuwar shirin USAID sannan gwamnatin kasar Amurka na mara mata baya a aiyukkan tallafin da take yi.

Share.

game da Author