SUN RUKUME: Sabon kwamandan ISWAP ya gillire kawunan kwamandojin da suka yi masa tawaye

0

Sabon kwamandan Boko Haram masu mugun tsatstsauran ra’ayi da kawance da ISIS, wato ISWAP, ya kara samun gindin zama daram akan jagorancin kungiyar ta ta’addanci, ta hanyar gillire kawunan manyan da suka yi masa tawaye su biyar.

Sabon kwamandan, mai suna Lawan Abubakar, wanda aka di sani da suna Ba Idrisa, ya gillire kawunan Shugabannin Majalisar Zartas da Shari’a da Hukunce-hukunce, wato Shura su biyar, cikin su kuwa har da tsohon kwamanda kuma shugaban Majalisar Shur’a din wanda ya hambaras cikin farkon watan Fabrairu, wato Abu Abdullahi Umar Al Barnawi, da ake kira Ba Idrisa.

Wata kwakkwarar majiya da ta san ciki da bai din abin da ke faruwa a cikin kungiyar mai zafi ta Boko Haram ce ta shaida daga Diffa, jihar Barno.

“Wannan ne kazamin fada mafi munin zubar da jinainai da kungiyar ta yi a takanin junan su. Ta kashe shugabannin da ta hambaras a cikin kankanen lokaci, kamar yadda masu binciken-kwakwaf fannin ta’addanci na jaridar PREMIUM TIMES da kuma Cibiyar HumAngle Media Foundation suka samu cikakken labari.

Yanzu dai Ba Lawan ya kama dalar mulkin sa ta hanyar zubar da jinainai, ko sauran sun ki, kuma ko da sun so.

An hambarar da Ba Idrisa, wato Albarnawy cikin watan Fabrairu tare da sauran shugabannin majalisar shura din sa su hudu.

Sai dai kuma ana ganin cewa kokarin neman zama daram kan mulki da kuma zugar makusantan wadanda aka kame din aka tsare, shi ne ya tinzira har aka yi tawaye.

An kashe Mohammad Bashir, Mustapha Jere, Ali Abdullahi, dawani hatsabibi mai suna Baba Mayinta. Yayin da har yau babu wanda zai ce ga sahihiyar ranar da aka kashe su ba, amma ana da yakinin cewa an gillire kawunan na su ne da a ranar 26 Ga Fabrairu ko 27 Ga Fabrairu.

Za a iya cewa ko dai kokarin ganin su na eman arcewa ne daga inda suke tsare, shi ne ya haifar da kisan na su. Domin a hasashe, Ba Lawan bai yi niyyar kashe su ba.

Turnukun musayar wutar da aka yi cikin daren Alhamis, 27 Ga Fabrairu, ya rayukan wasu shugabanni irin su Mustapha Krimina, wanda sai da daurin gindin sa ake nada shugaba.

Sai kuma Abu Musab, tsohon kwamandan da aka hambare cikin Maris, 2019 da kuma wani dan cikin shugaban Boko Haram na farko, Mohammed Yusufu.

Babu tabbacin ko harbin da aka yi masa ya kashe ko a’a.

Tabbacin tsoffinn shugabannin na da magoya bayaa cikin Bokoharam (ISWAP) ya kara fitowa fili ganin yadda sabon shugaban ya fito yay i musu jawabin cewa , “an kashe tsoffin kwamandojin ne saboda sun yi kokarin tserewa zuwa cikin kafirai su ji dadin yi mana makarkashiya daga can.”

Masu bibiyar al’amurran ISWAP na ganin hakan zai iya zama gaskiya, ganin yadda a baya lokacin da ya ke kan shugabanci, ya sassauto ra’ayin sa, inda ya ki kashe masu tseguntawa da tona asirin ISWAP.

Sai dai kuma ana Gnin cewa a karkashin shugabancin Ba Lawan, ISWAP za su kara kaimi wajen kame, hare-hare, da kisa bagatatan da kuma matsanaciyar keta da gallazawa.

Share.

game da Author