Sarkin wakan Sarkin Kano Naziru ya ajiye rawanin sa

0

Sarkin wakan sarkin Kano Muhammadu Sanusi, kuma fitaccen mawaki Naziru Ahmad ya sauka daga kujerar sarautar sarkin waka.

A takar haka da ya fitar, mawakin ya ce ya hakura da wannan sarauta daga yanzu.

Idan ba a manta ba tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi ne ya nada shi sarkin wakan Sarkin Kano tun bayan zaman sa sarki.

Naziru ya gode wa masarutar Kano bisa damar da ta bashi da ta nada shi sarkin wakain sarkin Kano.

Shima sakataren sarki Sanusi, Mujtaba Abba ya mika tasa takardar ajiye aiki da masarautar Kano.

Idan ba a manta ba gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya tsige sarkin Kano Muhammadu Sanusi a dalilin kin yi masa biyayya.

Share.

game da Author