• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    FALLASA RUFA-RUFAR HADI SIRIKA: Majalisar Tarayya ta nemi Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Nigeria Air

    Sanata Wamakko ya yi tir da kisan kiyashin da aka yi a tangaza, jihar Sokoto

    Atiku ya kafa gaggan lauyoyi 18, ya ce su tashi tsaye su ƙwato masa ‘nasarar zaɓen sa’ daga hannun Tinubu

    SHARI’AR ZAƁEN SHUGABAN ƘASA: Atiku ya zargi INEC ta ƙin ba shi kwafen bayanan zaɓe duk da ya biya haƙƙin Naira miliyan 6 kuɗin karɓar bayanan

    Gwamnatin Zamfara ta zargin tsohon gwamna Matawalle da sace motocin gwamnatin jihar da wasu kayan gwamnati

    Gwamnatin Kano ta rusa katafaren bene mai hawa uku da aka yi bisa filin gwamnati da Ganduje ya raba wa ƴan uwa da abokan arziki

    TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su  kai wa sojoji da mobal farmaki

    TSAUTSAYI: Yadda ‘yan bindiga suka ware da Lami Awarware da Haulatu bayan halartar taron rantsar da Uba Sani a Kaduna

    Sojojin Najariya sun kara ragargaza wa Boko Haram motocin yaki bakwai

    Sojoji sun dagargaza matatun mai 47 sun kama barayin mai 65 – Hedikwatar tsaro na kasa

    HAJJI 2023: Yadda jirgin maniyyatan Jigawa ya koma Kano ba shiri, bayan ya samu matsala cikin sararin samaniyar Kamaru

    GANAWAR TINUBU DA NLC: Ƙungiyar Ƙwadago ta ce a tilas a soke ƙarin kuɗin mai, an shammaci ‘yan Najeriya

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

    QATAR 2022: 2:1: Saudiyya ta kafa tarihin karya gadara da tutiyar buga wasan Agentina 36 a jere babu rashin nasara

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    BIDIYO: NAJERIYA @62: Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da mulkin Buhari a tsawon shekaru 7 da suka gabata

    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

No Result
View All Result

Sarki Sanusi: Bayan Kun Cire Shi Daga Sarauta, Wace Doka Ta Hana Ku Barshi Da ‘Yancin Sa! Daga Imam Murtadha Gusau

Premium Times HausabyPremium Times Hausa
March 13, 2020
in Ra'ayi
0
El-Rufai and Sanusi

El-Rufai and Sanusi

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Lallai dukkan kyakkyawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna yabon sa, muna neman taimakon sa, kuma muna neman gafararsa. Muna neman tsarin Allah da kariyarsa daga munanan ayyukkan mu. Duk wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, kuma duk wanda Allah ya batar babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa lallai babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammad, bawan sa ne kuma Manzon sa ne.

Salati da sallamawa, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) da alayen sa da sahabban sa da duk wanda yayi imani da shi kuma yayi aikin kwarai har zuwa ranar tashin kiyama.

Murtadha Gusau
Murtadha Gusau

Ya ku bayin Allah! Ku sani, lallai Allah Ya umarce mu da tsayar da adalci a bayan kasa, kuma ya sanar da mu cewa, da adalci ne sama da kasa suka tsayu. Kuma adalci shine ginshiki da tushen samun zaman lafiya da cigaba masu dorewa a cikin al’ummah. Sannan nagartattun malamai, salihan bayin Allah, irin su Shaikhul Islamu Ibn Taimiyya da Shehu Usman Dan Fodio da kanin sa Malam Abdullahin Gwandu duk sun shaida muna cewa:

“Allah yana taimakon daular da ta tsayar da adalci koda kafira ce, a yayin da Allah yake durkusarwa tare da karya duk daular da take zalunci koda Musulmi ne yake shugabancin ta.”

Kuma Allah Madaukaki Ya umurci Musulmi da su tsayar da adalci ta kowane hali, a inda Yace:

“Ya ku wadanda suka yi imani! Ku kasance masu tsayin daka domin Allah, masu shaida da adalci. Kuma kada kiyayya da wadansu mutane ta dauke ku akan ba zaku yi masu adalci ba. Kuyi adalci domin shine mafi kusa da takawa.”

Kuma Allah Yace:

“Kuma idan kun fadi magana to kuyi adalci, kuma koda ya kasance ma’abucin zumunta ne….”

Kuma Allah Ya sake cewa:

“Lallai Allah Yana umurninku da adalci da kuma kyautatawa…”

Kuma Allah Yace:

“Hakika mun aiko Manzannin mu da hujjoji bayyanannu, kuma mun saukar masu da littafi da ma’auni (na tsayar da adalci) domin mutane su tsayar da adalci tsakaninsu…”

Kuma Allah ya fada a Hadisil Qudusi cewa:

“Na haramtawa kai na zalunci, kuma na sanya shi ya zama haramun a tsakanin ku, saboda haka kada ku zalunci junanku.”

Ya ku Jama’a! Adalci shine, ajiye komai a inda ya dace, kuma shine bai wa kowa hakkinsa da Shari’a da doka suka tabbatar masa, ba tare da nuna ko wane irin banbanci ba. Kuma duk inda ake tsayar da adalci, to lallai zaka samu zaman lafiya, son juna, arziki, walwala, ci gaba da jin dadi a cikin al’ummah da tsakankanin jama’ah sun yawaita. A Musulunci, tsayar da adalci yana daga cikin manyan kyawawan dabi’u. Wannan ya nuna kenan duk inda Musulmi suke, indai har Musulmin gaskiya ne, da ma wadanda ba Musulmi ba adilai, shugabanni ne su ko ba shugabanni ba, zaka same su sun rungumi tsayar da adalci a tsakanin su.

Kuma Alkur’ani Mai girma ya bayyana muna karara cewa Allah ya umurci mutane da dukkan al’ummomi masu neman zaman lafiya da cigaba, su mu’amalanci junan su da kyakkyawar mu’amala, da tausayi da tsayar da adalci a duk halin da suka samu kansu a ciki. Kuma kowa yana sane da cewa, Allah yana son adalci, kuma yaki jinin zalunci, kuma baya son azzalumai.

Ya ku bayin Allah! Lallai ku sani, Allah ya wajabta wa dukkanin mutane, suyi kokari wurin ganin cewa an tabbatar da adalci a bayan kasa, domin samun zaman lafiya mai dorewa. Shi yasa Allah ya aiko Annabawa, kuma ya hado su da dokoki, domin su taimakawa mutane wurin tsayar da adalci. Wahayin da suka karba daga wurin Allah ya nuna hanyar da za’a bi a tsayar da adalci a cikin al’ummah. Misali, yiwa talakawa adalci, mazan su da matan su, kai hatta ma makiyan mu an umurce mu da muyi masu adalci.

Wajibi ne Musulmi da abokan zaman su, su hadu, su hada kai domin su dakatar da rashin adalci da zalunci a tsakanin su. Wannan aiki ne da Allah ya dora masu. Abu ne da sam bai dace ba Musulmi su zuba ido, su rungume hannuwansu, suna kallo ana tafka zalunci da rashin adalci ba tare da sun dauki kwakkwaran matakin da ya dace wurin tsayar da shi ba.

Annabi (SAW) ya fada a ingantaccen Hadisin sa, cewa:

“Ka taimaki dan uwanka, azzalumi ne ko wanda ake zalunta ne. Sai sahabbai suka ce: “Ya Manzon Allah, idan an zalunci dan uwanmu mun san ta yadda za mu taimake shi (wato mu kwato masa hakkinsa), to amma ta yaya za mu taimake shi idan shine azzalumin?” Sai Annabi (SAW) yace: “Ku hana shi aikata zaluncin, shine kun taimake shi.”

Bayan wannan, ya ku ‘yan uwa, kowa dai yana sane da abun da ya faru a Kano na cire Sarki Sanusi daga gadon sarauta. To alhamdulillahi, wannan yanzu ya riga ya wuce. Ina rokon Allah yasa hakan shine mafi alkhari, amin.

Yanzu abun tambayar shine, tun da kun sauke shi daga sarauta, to wace doka ce kuma ta hanaku ku bar shi da ‘yancin sa na walwala kamar kowa? Shin ba mulkin dimukradiyyah kuke ikirarin kuna yi ba? Shin ba kune kuke da’awa da ikirarin bin doka da oda ba? Shin yanzu muna cikin mulkin kama-karya ne na soja, ko kuwa muna cikin mulkin turawan mulkin mallaka ne, mulkin da Dan Adam baya da ‘yanci, sai yadda aka yi da shi?

Haba shugaban kasa. Haba manyan arewa. Haba shugabannin arewa! Yanzu irin abun da zaku sakawa wannan bawan Allah da shi kenan? Kuna kallo aka ci mutuncin sa aka sauke shi da karfi da yaji daga gadon sarauta, ba tare da bin wata doka ba, sannan kuma yanzu suna son su hana shi ‘yancin walwala.

Sun kai shi garin Loko a Jihar Nasarawa, daga nan yanzu sun mayar da shi garin Awe, ba tare da ganin alamun za ku ba shi hakkin sa da ‘yancin sa na Dan Adam da Allah ya ba shi ba, sannan kundin tsarin mulkin kasa ya ba shi. Ina dokar da kuke ikirarin kuna bi? Ko kuwa shi Sarki Sanusi bai cacanci ya amfana da wannan ba? Haba jama’ah, kuji tsoron Allah fa! Ku san da cewa za ku sauka daga kan mulki, kwana nawa ne, za ku dawo cikin talakawa? Kuma daga karshe sannan akwai mutuwa.

Mu ‘yan arewa, namu ne yake kan mulkin kasar nan, amma mun zama abun dariya a wurin abokan zaman mu. Mun zama abun tausayi. Idan aka taba Dan kudu guda daya, su duka za su taru akan nasu, su kare shi, su kwatar masa ‘yancin sa. Amma mu mun nunawa duniya cewa, daya daga cikin halayen mu shine, idan abu ya samu dayan mu za mu bar shi ne yaji da kan sa, in ma bamu koma gefe muna jin dadi da murnar abun da ya same shi ba, ko muyi dariya. Allah ya sawwake, amin.

Yau an wayi gari abun da ya kamata al’ummar Musulmi suyi basa yi, an wayi gari arna ne ma suke yi, shi yasa aka wayi gari suna kwasar muna ‘yan uwa suna mayar da su arna ta hanyar kyautata mu’ala, amma mu mun zama daga mu sai iyalan mu. Mun kasance sai surutu, sai girman kai, sai dagawa, sai hassada, sai ganin kyashin juna, sai turancin banza da wofi, mara amfani ga al’ummah.

Annabi (SAW) yace, idan aka taba dayan mu to kamar an taba mu ne. Sannan ya kamanta mu da cewa mu kamar gangar jiki guda muke, a wani wurin ya kamanta mu da gini, amma duk a banza!

Wallahi, wallahi, wallahi, Allah shine shaida, idan ba muyi komai akan sha’anin Sarki Sanusi ba, idan ba mu bi hanyar da ta dace, ta doka, wurin nema masa ‘yancin sa ba, to mun zama butulu, mun zama shirme, mun zama kaji masu ci su goge baki, la’akari da irin gudummawar da ya bai wa kasar nan, da ma arewa baki daya. Sannan mu sani, wannan abu da ya same shi yana iya samun kowanne daga cikin mu. Sannan wallahi, idan muka ci gaba da rungume hannuwa, muka ki taimakon junan mu, Allah ya sawwake, ba fata nike yi ba, sai Allah ya jarrabe mu da wasu bala’o’in da suka fi boko haram da kidnappers da banditry!

Yanzu don Allah ina amfanin ace wai namu ne yake shugabancin kasar nan? Amma arewa ta dada lalacewa. Zumuncin ‘yan arewa ya tabarbare. Mun rasa hadin kai. Mun rasa zaman lafiya. Mun zama shirme. Mun zama abun tausayi a kasar nan. Wannan wace irin al’ummah ce wannan? Mun zama kawai taron tsintsiya babu shara. Mun kasa iya fidda kitse wuta!

Wallahi ya zama wajibi mu shiga taitayin mu. Allah yana kallon duk abunda muke yi, kuma yana sane da komai. Sannan mu sani, Sarki Sanusi ya wuce muyi masa haka. Yanzu don girman Allah irin sakayyar da zamu yi masa kenan? Haba jama’ah. Yanzu wannan abun da ya faru da shi, don Allah zamu so ya faru da mu?

Sannan in ba raina hankalin mutane ba, wace dokace a cikin dokokin kasar nan, ko dokokin addinin mu, tace idan an cire Sarki a wulakanta shi, a tauye masa hakki, a hana shi ‘yancin sa na walwala kamar kowa? Idan akwai dokar a fada muna ita don Allah mu san ta!

Wallahi a iya sani na, babu wata doka irin haka in banda kama-karya kawai da zalunci!

Ina lauyoyin mu suke ne? Ina kungiyoyin da ke fafutukar kare ‘yanci da hakkin Dan Adam ne? Alhamdulillah, koda yake naga wasu kungiyoyi, kamar CISLAC da SERAP da mutane irin Deju Adeyanju da Dr. Aliyu Tilde sun dan yunkuro akan wannan.

Wallahi wannan abun da ya faru babban abun kunya ne ga dukkanin Kanawa na gaskiya da ‘yan arewa baki daya.

Ba wani abun kunyan da zai wuce wannan abun da ya faru a Kano. Duk wani abin kunya da zai faru kuma, a bayan wannan ne.

Wallahi ko shakka bana yi cewa da Bola Tinubu yace a kyale Sarki Sanusi kar a cire shi, to wallahi za’a bar shi. Amma ga shi duk fadin arewa kaf sun ki jin maganar kowa.

Don Allah wane gwamna ne a kudu ya isa ya cire Oba na Legas, ko Oba na Benin, ko Obi na Onitcha? Ai kaga babu shi. Sannan wanne dan arewa ne ya isa yasa baki a cikin al’amurran cikin gida na wata jiha a kudu? Kaga babu shi.

Amma mu tun daga zaben farko da aka yi a Jihar Kano, har zuwa inconclusive, har zuwa cire Sarkin Kano, mun ga yadda bakin mutane daga wasu jihohi suke ta sarrafa al’amurran mu.

Yanzu a wurin gwamnonin mu, ya nuna kenan babu wani mai mutunci ko mai fada a ji a Kano ko a Arewa. Idan ma akwai toh ba ya fadar ko idan ya fada ba’a ji.

Yanzu idan lokacin zabe yazo, wanne irin campaign za’a yi wa Kanawa da ‘yan arewa na neman kuri’ar su?

Ya Allah, ka sakawa Sarki Muhammadu Sanusi II da alheri, Ya Allah ka fisshe shi kunyar makiya, Ya Allah kasa abun da ya faru shine mafi alheri a gare shi, da mu duka, amin.

Amma dai gwamna Ganduje ya kwana da sanin cewa, za’a rika tunawa da shi ne a matsayin gwamnan kama-karya tsawon tarihin Kano. Sannan ya sani, duk makusantan shi za su guje shi bayan mulkin shi, har sai ya nemi makwabta da zasu bashi gudummawa ya rasa. Sannan gwamna Ganduje zai gagara nada magajin shi akan gadon mulkin Jihar Kano, sannan kuma zai kasa shiga cikin mutane saboda kunyar matakan da ya dauka munana. Kuma akwai yiwuwar a zabe mai zuwa, muna raye ne ko mun mutu, jam’iyyarsa ta APC zata fadi a siyasar Kano mai zuwa, muddin dai shugabannin jam’iyyar basu karbi ragamar ta daga hanun sa ba.

Sarki Sanusi dai yayi nashi ya gama, domin duk duniya ta shaida cewa ya rike gaskiya. Kuma ita gaskiya abun rikewa ce a wurin kowane nagartaccen mutum. Mutum mai gaskiya kuwa koda yaushe daban yake a cikin al’ummah, kuma abun duniya bai tsone masa ido ba. Yanzu gashi nan dai, duk yadda yake son sarautar nan, ya hakura, ya bar ta, dalilin gaskiyar da ya rike. Tun farkon rigimar shi da Ganduje akan maganar ciwo bashi, ya san inda za ta kai shi, amma ya zabi gaskiya. Don haka Allah yana tare da mai gaskiya a duk inda yake. Masu hikimah sun ce:

“Allah bai taba kulle maka wata kofa ba, face ya bude maka wata kofar wadda ta fi ta fadi da yalwa.”

Sannan dukkanin masoya Sarki Muhammadu Sanusi II sun san cewa, da yardar Allah, wannan canji ci gaba ne a gare shi. Muna nan muna ta addu’a. In Shaa Allahu, sauki na nan tafe!

Ya Allah, muna tawassali da sunayenka tsarkaka, ka tausaya muna, ka karbi tuban mu, ka azurta mu da hakuri, juriya, jajircewa da ikon cin jarabawar ka a ko da yaushe.

Ya Allah, kayi muna gafara, ka shafe dukkan zunuban mu, don son mu da kaunar mu ga fiyayyen halitta, Annabin rahmah (SAW).

Ina rokon Allah ya kyauta, ya kawo muna mafita ta alkhairi, amin.

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Tags: NewsPREMIUM TIMESSanusiSarki
Previous Post

An gurfanar da saurayin da yayi wa Akuya fyade a kotu

Next Post

Gwamnati za ta ciwo bashin Naira biliyan 45 domin saka yara a makaratun boko – ministan ilimi

Premium Times Hausa

Premium Times Hausa

Next Post
Adamu Adamu

Gwamnati za ta ciwo bashin Naira biliyan 45 domin saka yara a makaratun boko – ministan ilimi

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • FALLASA RUFA-RUFAR HADI SIRIKA: Majalisar Tarayya ta nemi Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Nigeria Air
  • Sanata Wamakko ya yi tir da kisan kiyashin da aka yi a tangaza, jihar Sokoto
  • CIRE TALLAFIN MAI: ‘Yan Najeriya na dandana tsadar kayan abinci da motocin sufuri
  • TASHIN HANKALI: Saboda lalacewa yanzu, har Nas-Nas na fede mutum asibitoci
  • Dalibai 350 muke da amma malamai uku kacal ke karantar dasu a makarantar mu – Mazauna kauyen Gabchyari, Jihar Bauchi

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.