Tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya maka sufeto Janar din ‘Yan sanda, shugaban Hukumar Tsaro SSS da Antoni Janar din Najeriya bisa tsare shi da ke yi bayan tsigeshi da gwamnan Kano Ganduje yayi.
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya tsige sarki Sanusi daga sarautar Kano ranar Litini inda ya musanya shi da Sarkin Bichi kuma tsohon dan sarkin Kano marigayi Ado Bayero, Aminu Ado.
Bayan tsige sarki Sanusi sai aka kore zuwa Kasar Awe domin ya ci gaba da zama.
Sanusi ya garzaya kotu ranar Alhamis domin mika kukan sa da kuma neman kotu ta tilasta wa mahukunta su kyaleshi ya ci gaba da watayawar sa kamar yadda dokar kasa ta bashi dama.
A takardun karar da Sanusi ya shigar babban kotun a Abuja, mai lamba FHC/ABJ/CS/357/2020, ya roki kotu ta kwato masa hakkin sa kamar yadda dokar kasa ta bashi na iya zirga-zirga da wataya wa banda zuwa garin Kano har sai bayan haka an yanke hukuncin karar da ya shigar.
Lauyoyi da dama sun bayyana cewa ba a yi wa Sanusi adalci, rashin jin nasa bayanan, aka tsige shi. A dalilin haka kuwa doka ba ta bada daman kuma a hana shi walwala ba tunda dai shima dan kasa ne kuma yana da ‘yan cin sa.
Discussion about this post