Tsohon gwamnan jihar Legas, kuma jigo a jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya bayyana cewa yana tare da shugaban jam’Iyyar Adams Oshiomhole 100 bisa 100 a wannan lokaci da wasu marasa kishin jam’iyyar suka kunno masa wuta.
Tinubu ya Kara da cewa wasu tun yanzu sun bugu da giyar siyasar 2023 sun tangal-tangal maimamakon maida hankali wajen ganin jam’iyyar ta iya cika alkawuran da ta dauka wa ‘yan Najeriya.
” Yanzu dai an samu an iya tattare cutar coronavirus daga yaduwa a Najeriya, sai dai kuma akwai wata cutar da tafi coronavirus da ke cin mutane kamar wutaddaji, wannan cuta itace cutar guguwar siyasar 2023 da ta kunno Kai tun yanzu.
” Yanzu wasu sun feke wukaken su sun fara zazzaro idanu suna neman wanda zasu guntule wa kafafu, saboda siyasar 2023. Su fa suna so ne tun a 2020 dinnan a karkare ta kawai.
” Yanzu-yanzu kawai suke so ayi ta ta gama kowa ya san gaban sa. Abu da saura shekara uku tukunna kafin ma a buga gangar siyasa a kasar nan. Suna nan suna nuna su ne masoyan Buhari, bayan kuwa suna yin kwance-kwance suna sarar gwamnatin, suna dildilamata guba ta ko-ina don son rai da neman kujerun mulki.
” Wannan makirci da suke shiryawa ba zai kaisu ko Ina ba, domin jirgin da suke so su tuka ma ba a ko gina titin ta ba.
” Idan akwai hankali, na tsuwa a tare da irin wadannan mutane, ya kamata su san cewa siyasa na da lokaci.
” Bai kamata ace wai yanzu za a fito ana sukan shugaban jam’iyyar APC ba domin wasu gazawarsa. Idan da za ayi masa adalci, ya taka rawar gani matuka sannan akwai Inda yayi kuskure. Amma ay shi ba waliyyi bane da za ace ba zai taba yin kuskure ba, idan ko ba haka ba ashe da kwata-kwata ba za a taba yin shugaba a jam’iyyar ba, idan Wanda ba ya kuskure ake so.
” Kowa ya san cewa Oshiomhole da gwamnan Edo Obaseiki ba su ga maciji. Amma kuma jam’iyyar na kokarin sasanta su. Maimakon a bari a ga karshen yadda sasantawar zai kasance, sai wasu ‘yan siyasa suka dukufa wajen daukar wannan dama da yin amfani da barakar domin dagula komai duk saboda 2023.
” Sannan kuma wasu har kotu suka je duk da dokar jam’iyyar APC bata amince da haka ba. Ba a gama yin amfani da duka hanyoyin da jam’iyya ta samar ba tukunna. Hakan ba daidai bane.
” A rashin hankali kuma wani ma har kiran taron uwar jam’iyya yayi wai shine shugaban jam’iyyar a yanzu. Mun sani wasu ne da ke ganin suna da karfi a gwamnati suke zuga shi da kila yi masa alkwarin wani kujera ko wani abin.
” Masu shirya wannan makirci na yin haka ne don sun ga cewa tabbas shugaban jam’iyyar, Oshiomhole zai zamo musu kashin kifi a wuya a 2023.
” Wasu ne kawai ke so su yagalgala jam’iyyar, su kawo rudani a ciki sannan su dawo daga baya su yi amfani da haka wajen neman kujerun na siyasa. Wannan babban rashin hankali ne da bacin rai.
” Da yawa daga cikin mu mun yi gumi, Sau da yawa har hawaye mun zubar, wasu lokuttan mu kan kasa bacci duk don mu gina wannan jam’iyya Amma yanzu duk sadaukarwar da mu kayi ya zama a banza ke nan?
” Mun kafa kuma muka gina wannan jam’iyya ba don burin mu ba kawai, mun gina ta ne domin kawo canji mai nagarta a kasar nan. Wadanda suke so su lalata wannan tafiya su sani cewa jam’iyyar ba jam’iyyar son rai bace. Ka zama Dan jam’iyyar nan kawai ya wuce ace kawai don kasa mu wani abu ne na siyasa.
” Wadanda wannan annobar 2023 ya shiga jinin su tun yanzu su sani suna tozarta Buhari ne da gwamnatin sa. Hada hannu za a yi aga yayi nasara ba wai su koma suna maganar 2023 wadda har yanzu ba a cika shekara daya cur da aka rantsar da sabuwar gwamnati ba.
” Ni dai na fadi nawa, sauran ya rage wa masu kunnen basira su saurara sanna su yi amfani da abinda na fadi.
” Ko mun ki ko mun so, 2023 zai zo wata rana, kuma koma me muke so za ayi a wuce. Abinda ya kamata mu maida hankali a kai shine ganin Shugaba Buhari ya yi nasara a abubuwan da ya sa a gaba na gyara Najeriya. Sai dai kuma duk da haka wadanda giyar mulki ke rudin su ba za su dai na ba. Da karfin tsiya suna so tun a yanzu a yamutse kawai domin su burin su kawai siyasar su, ba Buhari ba kuma ba ci gaban jam’iyya ba.