Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa wasu mahara sun kashe mutane biyu a kauyen Galawa dake karamar hukumar Bagwai.
Wannan abin tashin hankali da ban tsoro ya faru da karfe 10:30 na daren Litini.
Kakakin ‘yan sandan jihar Kano Abdullahi Kiyawa ya sanar da haka wa manema labarai inda ya kara da cewa maharan sun harbe mutane uku, biyu sun mutu a asibiti.
“Maharan sun shigo suna barin wuta ta ko-ina, mutane kuma suka faffalla da gudu kowa ya yi ta kansa. A haka ne suka harbe mutane uku.
“Guda daya din da ya rage ya fara samun sauki a asibiti.
Kiyawa yace Muhammed Sani ma’aikacin cibiyar kiwon lafiya na matakin farko da wata Balaraba Sani ‘yar wani dan siyasa duk a kauyen ne suka rasu.
Kwamishinan ‘yan sanda Habu Sani ya aika da jami’an tsaro domin farautan wadannan mahara.
Idan ba a manta ba a wannan mako ne mahara suka kashe mutane sama da 50 a kauyuka shida dake kananan hukumomin Giwa, Birnin Gwari da Igabi ranar Lahadi a jihar.
Ire-iren wannan hare-hare ya kazanta a yankin Arewacin kasar nan.
A ziyarar jaje da ya kai wadannan kauyuka, gwamna El-Rufai ya nuna takaicin sa game da abinda ya faru sannan ya ce kwazon gwamnati ya gajarta matuka wajen samar wa mutane tsaro a kasar nan.
El-Rufai ya roki mutanen jihar Kaduna da su yi hakuri su yafe wa gwamnati a dalilin rashin iya samar musu da tsaro a fadin jihar.