Wakilin hukumar gudanar da bincike kan ingancin amfanin gona (ICRISAT) Hakeem Ajeigbe ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba Najeriya za ta fara fitar da dawa zuwa kasashen waje.
Ajeigbe ya fadi haka ne da yake hira da PREMIUMTIMES a jihar Kano.
Yace gwamnati ta kammala shiri tsaf domin ganin Najeriya ta fara siyar wa kasar Britaniya markadadden dawa.
“Kasar za ta yi amfani da shi wajen sarrafa lemon maltina, alawar chakulat, biskit da dai sauran kayan kwadayi da marmari.
“Mafi yawan mutane na da sanin cewa ana amfani da dawa wajen yin kunu da giya ne kawai da tuwo. Baa ga wadannan abubuwa akwai abu da dama da ake yin su da dawa.
“A yanzu mun horas da mata dake kauyuka yadda ake yin gurguru da dawa sannan da yin garin dawa domin soya fanke da sauran abinci.
Ajeigbe yace gwamnatin Najeriya ta karkata wajen inganta amfani da dawa ne ganin yadda mutane da dama suka daina cin dawa a kasan.
“Yanzu manoma sun koma ga noman shinkafa da masara inda hakan ya sa babu abincin da mutum zai ci musamman a arewa da babu shinkafa ko masara a ciki.
“Cin irin wannan abinci ne ya sa ake yawan kamuwa da ciwon siga, yawan kiba da sauran cututtuka.
Ajeigbe ya yi kira ga mutane da su rika cin kayan abincin da suke inganta karfin garkuwar jiki musamman kayan lambu da ganyayyaki.