Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan, ya nuna rashin jin dadin sa, tare da bayyana cewa Najeriya ba ta tabuka komai a fannin binciken bunkasa harkokin noma a kasar nan.
Ya ce duk da matsalar kuncin talauci da fatara da koma bayan inganta harkokin noma, amma Najeriya ba ta tabuka abin a yaba a fannonin bunkasa binciken habbaka noma.
Sanata Lawan ya yi wannan kakkausan korafin ne a Majalisa lokacin da ake bibiyar kudirin kafa Hukumar Bunkasa Binciken Harkokin Noma, domin a yi wa dokar da ta kafa hukumar kwaskwarima.
“Maganar gaskiya babu wani katabus wajen bunkasa harkokin noma da kuma kirkiro hanyoyin bunkasa kayan noman.
“Abin takaici ne a kasa kamar Najeriya a ce manoma na shanya tumatir a gefen kwalta ko a kan tsandaurin kasar da suka share, su na baza tumarir domin ya bushe. Wannan abin kunya ne, kuma abin takaici.”
Najeriya ta ware naira bilyan 183.08 domin kashewa a fannin noma a shekarar 2020, wanda kuwa kashi 1.73 bisa kashi 100 ne na kasafin naira tiriliyan 10.608 da za a kashe a kasafin na 2020.
Najeriya na da cibiyoyin bunkasa harkokin noma har 23 a kasar nan. A kan haka ne Shugaban Majalisar Dattawa ya ce kamata ya yi a ce tuni manoman kasar nan su na samun kayan ayyukan bunkasa noma na zamani wadatattu.
“Abin haushi da takaici, duk da dimbin alhairan da ake samu a fannin noma da kuma samar da kudaden raya tattalin arziki har kashi 23 bisa 100 da fannin noma ke yi, ga kuma kudaden da ake narkawa da sunan tallafin manoma, har yanzu ba a tabuka abin kwarai wajen bunkasa noma ta yadda manoma za su rika gudanar da harkokin noma a zamanance, har ya zama kacokan abin dogaro wajen bunkasa Samar d abinci da kuma inganta tattalin arziki.” Inji Sanata Lawan.
Discussion about this post