Na kamu da Coronavirus – Gwamnan Makinde na Oyo

0

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana cewa sakamakon gwajin jinin sa ya nuna cewa shima ya kamu da cutar coronavirus.

Makinde ya bayyana haka a shafinsa ta Tiwita inda ya ce gwajin jinin sa ya nuna cewa shima fa ya kamu.

” A dalilin haka zan koma daki in killace kai na zuwa in warke. Ina kira ga ‘yan jihar Oyo su mai da hankali su bi doka. Su tsaya a gida sannan su mai da hankali.”

Makinde ne gwamna na uku cikin gwamnonin Najeriya da suka bayyana sun kamu da cutar a kasar nan. Akwai gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, sai kuma yanzu gwamnan Oyo.

Share.

game da Author