Na kamu da coronavirus – El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya sanarwa mutanen jihar cewa shima ya kamu da cutar coronavirus.

Ya bayyana haka a wata takaitacciyar jawabi da yayi wa mutanen jihar Kaduna da yammacin Asabar.

” Bayan an yi gwajin jini na, hukumar NCDC ta tabbatar da na kamu da cutar coronavirus. Daga yanzu zan ci gaba da zama kadaici a killace, likitoci suna duba ni.

” Ina so in sanar wa mutanen jiha ta cewa zan ci gaba da ayyuka a inda nake, sannan mataimakiyar gwamna zata ci gaba da duba ayyuka a jihar.

El-Rufai ne mutum na farko da ya kamu da cutar a jihar Kaduna.

Share.

game da Author