N-POWER: An dauki matasa 400,000 a karkashin Shirin Inganta Rayuwar Marasa Galihu – Minista Sadiya

0

Gwamnatin Najeriya ta dauki matasa har 473,137 a karkashin Shirin Inganta Rayuwar Marasa Galihu.

Wannan ikirari ya fito ne daga bakin Ministar Ayyukan Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Al’umma, Sadiya Umar.

Sadiya ta yi wannan bayani ne a lokacin Kwamitin Majalisar Tarayya mai kula da Shirin Yaye Fatara da Talauci ya kai mata ziyara a ofishin ta.

Ministar ta ce dama tun da farko an kirkiro Shirin N-Power ne kacokan domin samar wa matasa ayyukan yi.

Cikin Fabrairu ne PREMIUM TIMES ta buga labarin wani garambawul din da Ma’aikatar Ayyukan Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Al’umma ta ce za ta yi wa shirye-shiryen NSIP garambawul.

“An kirkiro N-Power domin inganta rayuwar matasa, ta hanyar sama musu ayyukan yi ta yadda za a habaka fannonin ilmi, noma, lafiya da kuma haraji.

” Kudirin wannan gwamnatin shi ne a sama wa matasa akalla 500,000 ayyukan yi a fadin kananan hukumomi 774 na fadin kasar nan.”

Ta yi karin bayani a kan shirye-shiryen inganta al’umma ta hanyar ba su lamunin kama sana’o’in yau da kullum domin dogaro da kai.

Ta kara yin bayanin cewa har yanzu gwamnati na cigaba da bayar da tallafin rage radadin talauci na naira 5,000 da ke rabawa duk wata ga marasa galihu.

A na sa jawabin, Shugaban Kwamiti, Abdullahi Silame, ya yaba wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, saboda kokarin ci gaba da gudanar da shirin da ake yi.

Share.

game da Author