Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Dukkan kyakkyawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, mai kowa mai komai. Mamallakin komai. Mai bayar da mulki ga wanda yaso. Mai kaskanta wanda yaso. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW), da iyalan sa da Sahabban sa baki daya.
‘Yan uwa na masu girma, ku sani, yana da wahala a samu wasu ‘ya ‘yan gidan sarauta a arewacin Najeriya kaf da suke yakar kan su, suke kin junan su, suke neman su cuci kansu da kansu, kuma su rusa wahalar da magabatan su suka yi, kamar ‘ya’yan sarautar Kano, musamman zuri’ar masu Martaba Sarki Sanusi na I da Sarki Ado Bayero. Abun bakin ciki, abun takaici, wallahi wadannan mutane basu kaunar junan su. Sannan basu kaunar ganin ci gaban dorewar abun alkhairin da magabatan su suka shuka. Abun da kawai yake gaban su shine, yaya za’a yi su hau wannan karaga ta sarautar Kano, da karfi da yaji, kuma ko ta halin kaka, ko da kuwa za su cutar da junan su ne, kuma ko da za su rusa duk wani zumunci da ke tsakanin su. A cikin zuri’ar Sarki Sanusi na I, wallahi abun da ‘ya ‘yan Galadiman Kano, Abbas Sanusi suke yi, irin su Isa Sanusi, Abdullahi Abbas da kuma Ujudud Sanusi, na kokarin ganin sun hada kai da wasu kazaman ‘yan siyasa, domin aci mutunci, tare da rusa ayukkan da magabatan su suka yi, abun babu kyau. Suna kashe kudi, suna tsafe-tsafe, suna aikata duk wani nau’i na bita-da-kulli, domin ganin sun cimma wannan buri na su. Wadannan mutane sun ki jinin Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, sun yarda domin su ga bayan sa, su aikata komai. Sun hada kai da wasu daga cikin ‘yan ‘yan bawan Allah, mutumin kirki, Mai daraja, wato Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, da kuma wasu kazaman ‘yan siyasa, wadanda babu abun da za su rasa, kuma babu wata hasara da zasu yi idan har an rusa Masarautar Kano mai dimbin tarihi da daraja.
Wannan adawa da suke yi da Sarki Sanusi, ba fa wani laifi yayi masu ba, a’a, kawai su a ganin su, wai Allah yayi kuskure da ya ba shi ikon hawa gadon Sarautar Kano. Suna ganin Allah da ya bashi bai yi daidai ba. Suna ganin bai cacanci ya hau ba saboda mahaifin sa bai yi Sarki ba, duk da cewa kakansa yayi, kuma shi din jinin sarautar ne, kuma ma shi ya fisu dacewa da cacanta a duk cikin zuri’ar Malam Ibrahim Dabo. Suna ganin wai sun fi shi dacewa da cancanta, don haka dole ne ya sauka su hau! Wannan irin rudi da wahayin shaidan shine ya kai su ga wannan bakar adawa da suke yi da shi.
Wadannan mutane, sun sha alwashin sai sun tozarta Masarautar Kano. Sun sha alwashin ko nawa za su iya kashewa domin su cimma nasara a wannan bakin buri nasu. Har ma mun ji daga majiya mai tushe cewa, wani daga cikin su ya bayar da gudummawar naira biliyan biyu domin ganin an cire Sarki Sanusi an nada shi a matsayin Sarki. Alhali sun manta da cewa, Allah da jama’ar jihar Kano na tare da wannan bawa na shi.
A kokarin da suke yi na rusa wannan Masarauta mai daraja, da rusa gumin iyayen su da kakannin su da magabatan su, sun jawo an wayi gari wasu banzayen mutane, ‘yan iska, marasa mutunci, wadanda ba ‘ya ‘yan kowa ba a Kano, suna zagi da batanci ga wannan Masarauta da kuma Sarki Muhammadu Sanusi II. An wayi gari sun mayar da dandalin soshiyal midiya, dandalin baje-kolin cin mutuncin Sarki Sanusi, saboda su ba ‘ya ‘yan mutunci ba ne, kuma ba su san girman manya ba. Wai har wani wawa yake shiga gidan radio yana cewa da ace shine gwamna Ganduje da yanzu aikin gama ya gama. Kuma wani daga cikin zuri’ar Dabo yake fada a gidan radio da duk duniya ta ji shi, yana cewa wai shi in dai har za’a cire masu Sarki Sanusi II, to komai na Masarautar ya yarda a rusa shi, a kawo karshen shi!
Yanzu don Allah su ‘ya ‘yan Galadiman Kano, Abbas Sanusi, da duk duniya ta shaida cewa sun amfana matuka da Sarki Sanusi, suna nufin gwamna Ganduje son su yake yi tsakani da Allah? Yanzu don Allah suna nufin idan gwamna ya cire masu Sarki Sanusi ya taimake su ke nan? To idan wannan shine tunanin su, to wallahi su sani, sun tabka babban kuskure. Kuskuren da sai sun yi nadama da dana-sani a kan sa!
Kuma ya kamata zuri’ar Dabo su sani, idan har suka ci gaba da bayar da dama domin aci mutuncin ‘yan uwan su, saboda son zuciyar su, to wallahi abun da zai faru shine, yin nadama da dana-sani, da kukan bakin ciki, domin abun da kuka bayar da dama aka yiwa Dan uwan ku, to tabbas wata rana zai dawo kan ku.
Kuma wannan abu da suke yi kada suyi tsammanin cewa suna cutar da Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ne, a’a, wallahi sam ba haka bane, kan su suke rusawa. Sannan kuma ma hakan babu abun da yake karawa Sarki Sanusi illa Martaba da daraja da kauna da soyayya a wurin al’ummah.
Sannan su sani, wallahi ba wai sun fi kowa bane, a’a, kawai albarkacin wannan sarautar ne suke ci, kuma ita ce gatan su. Sarautar nan ita ce tayi masu komai na rayuwa. Sarautar nan ita ce ta saka su a makaranta, ita tayi masu aure, ita ta basu gida, ita ta basu aikin da suke takama da shi suna rike kan su da shi, kuma ita ce ta martaba su kuma ta daga darajar su har duniya ta san su. Don haka su sani, da zarar an wayi gari ta lalace, to su ba kowa bane, domin zasu zama daidai da sauran mutane!
Kuma idan suka yi sakaci, suka ci gaba da hada kai da makiyansu, har suka yi sakacin da suka bari Masarautar nan ta lalace, to su sani, ba Martabar Sarki Sanusi ce ta lalace ba, a’a, wallahi sune suka lalace. Sannan kuma tsiya da gaba da kiyayya da talauci da rashin girma suyi ta bibiyar su har kabari!
Gwamna Ganduje baya ganin mutunci da darajar wannan Masarauta mai dimbin tarihi da daraja. Ya sha alwashin sai ya rusa ta. Duk take-taken sa da maganganun sa sun nuna hakan. Wannan adawa da Ganduje yake yi da wannan Masarauta, ta samo asali ne domin kasancewar sa daga zuri’ar bagobiri. Domin shi ba bafulatani bane, bagobiri ne, bawan Fulani, shi yasa yake jin yaren fulatanci. Yana ganin tun da fulani sun bautar da su to sai ya rama. Ya tsani Shehu Dan Fodio da zuri’ar sa, shi yasa ya fada a wani lokaci cewa, jihadin Dan Fodio kama-karya ne kawai da zalunci. Dalilin da yasa ke nan yake so ya rusa zuri’ar Dabo. Kuma ya fada a wani lokaci cewa, tutar Shehu Dan Fodio ba komai ba ce. Kuma ya fada cewa tarihin Dan Fodio ba ya da banbanci da tsafe-tsafe ko tatsuniyar tsumburbura! Amma duk da haka wai aka wayi gari wasu daga cikin zuri’ar Dabo, dakikai, jahilai, suna goyon bayan sa. Sun hada kai da shi wai su a cire masu Sarki Sanusi, suna ganin idan an cire shi su zasu hau gadon sarautar.
Kuma ta wani bangaren, su wadannan dakikai daga cikin zuri’ar Dabo, sun manta da cewa, gwamna yana kokarin daukar fansar cire mahaifinsa ne daga dagaci da aka yi, saboda yaci kudin haraji, kudin talakawa. Inda da tunani, ta yaya wadannan mutane daga zuri’ar Sarki Sanusi na I, za su hada kai da mutumin da yake nema yaci mutuncin magabatan ku? Ku duba don Allah yadda ‘ya ‘yan Galadiman Kano, Abbas Sanusi suka hada kai da Ganduje, wai suna tunanin zai basu Masarautar Kano saboda dakikancin su.
Wallahi Ganduje ya cutar da al’ummar jihar Kano, kuma yana kan cutar da su. Ya jefa Kanawa cikin kunci da damuwa da zaman dar-dar. Ya zama yanzu mulkin Kano kawai shine, yaya za’a yi a cire Sarki Sanusi daga sarauta. An takura wa mutane. Babu aikin ci gaba, sai shirme. Wai abun mamaki, wai har wata jarida take bashi wai wata lambar girmamawa, domin basu san abun da ke faruwa a Kano ba. Ko da yake, wannan lambar girmamawa wani lokacin sayen ta ake yi da kudi.
Duk mai hankali yasan da cewa jihar Kano a tsaye ta ke cak sanadiyyar wannan rikici. Don haka jama’ah wallahi ya zama wajibi mu cire son zuciya mu dukufa da yin addu’ar Allah yayi muna maganin dukkanin masu rura wutar wannan fitina ko su waye, kuma a ko’ina suke.
An zagi fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) a Kano, anci mutuncin sa, amma bamu ji gwamnati ta dauki wani kwakkwaran mataki na azo a gani ba, sannan ‘yan majalisar jihar Kano ba su yi doka akan kare martaba da mutuncin Annabi (SAW) ba, amma wai sun karbi kwangilar cire Mai Martaba Sarki son rashin kunya. An kirkiro wata tatsuniya, wata karya, cewa wai wasu sun kai karar Sarki akan yaci mutuncin addini da al’adar mutanen Kano. Wadannan mutane babu su, kuma babu wanda ya san su. Wannan wallahi tatsuniya ce kawai, wasan kwaikwayo ne. Mutanen anguwar ma da aka ce sun kai karar Sarkin, sun fito fili karara, sun shaida wa duniya cewa sharri aka yi masu, sunce su basu san da wannan tatsuniya ba!
Wai har wani marar kunya, wai shi Ali Baba Yakasai, yake yiwa duniya karya cewa wai duk Kano babu wanda hankalin sa yake yashi idan aka zagi Manzon Allah (SAW) irin gwamna Ganduje. Kun san wannan magana karya ce. Idan har gaskiya ne me yasa basu dauki wani kwakkwaran mataki ba, sai suka buge kawai da maganar cire Sarki?
An wayi gari basu ganin girman duk wani babba a jihar Kano da wajen ta. Sun kira dattijai masu daraja da dattijan wukari. Malamai, Sarakuna da duk wani mutum mai mutunci sun zama ba su da kima a wurin su. Dan siyasa ya shiga radio ya keta alfarmar su ba komai bane. Wallahi irin wannan bakar siyasar ta rashin ganin girman manya ba za ta haifar muna da mai ido ba.
Sannan sun kirkiro wata tatsuniya, wai Sarki ya sayar da filayen Masarauta da ke darmanawa ya cinye kudin, don haka za su gayyace shi wai yayi bayani. Kai ka san wallahi wadannan mutane suna wasa da hankalin al’ummah. Ta yaya mutumin da ya rike baitul malin kasa baki daya (Central Bank of Nigeria) ba’a zarge shi ba, ba’a ce yaci kudi ba, wai sai ‘yan canjin Masarauta da ba komai ba? Alhamdulillahi, kotu ma ta dakatar da wannan wasan kwaikwayon.
Amma duk da cewa kotu ta dakatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa daga bincike ko gayyatar Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, gwamna Ganduje ya dage, yace shi ba zai bi doka ba, su zasu ci gaba da makircin su na cire Sarki.
A cikin satin nan gwamna Ganduje shi da mukarraban gwamnatin sa sun yi ta taruruka daban-daban a birnin Abuja domin kammala shirin su na cire Sarki. Kuma sun sha alwashin ba zasu bi umurnin kotun ba.
Yau litinin, 09/03/2020, sun kira wani taro anan Kano, a inda za su zartar da hukuncin karshe akan wannan al’amari. Kuma a wannan taro da zasu yi a gidan gwamnatin jihar Kano, sun gayyaci Mai Martaba Sarki. Kuma duk wannan abu da ke gudana, shugaba Buhari yaki cewa komai akai!
Daga karshe, ina mai tunatar da mu cewa, Manzon Allah (SAW) ya roki Allah, yayi addu’a mai zafi cewa:
“Ya Allah duk wanda ka bawa shugabancin al’ummata, sannan ya tausaya masu, Ya Allah shima ka tausaya masa. Ya Allah Duk wanda ka bawa mulkin al’ummata, sannan ya kuntata masu, Ya Allah shima ka kuntata masa.”
Sannan Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, Allah yana tare da kai. Ina rokon Allah ya kara maka daukaka da lafiya, da fatar Alkhairi a gare ka koda yaushe, da dukkanin Sarakunan mu da Masarautun mu masu daraja.
Ina rokon Allah ya kyauta, kuma ya kawo muna mafita ta alkhairi, amin.
Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.
Discussion about this post