‘Yan uwan tsohon direban Dan majalisar Tarayya da mahara suka kashe a titin Kaduna zuwa Birnin Gwari, Ibrahim Idris sun shaida wa PREMIUM TIMES,cewa mahara dauke da makamai sun farwa wa motan hayan da Dan uwansu ya shiga daga Kaduna zuwa Birnin Gwari, inda suka kashe sannan suka yi garkuwa da wasu da dama.
Abubakar Garba, da ya yi magana da wannan jarida ya ce baya ga kashe Dan uwan sa da suka yi, mahara sun arce da wasu dalibai uku, biyu maza da mace daya.
Wani da ya tsira ya bayyana cewa babu maharan sun fito titi tun da misalin karfe 4 na yamman ranar Asabar ne suka bude wa motan wuta.
Haka kuma an samu rahoton sun sake fitowa a wannan hanya sun tare mutane kuma sun yi garkuwa da wasu.
Kakin rundunar ‘Yan sandan jihar Kaduna Mohammed Jalige ya bayyana cewa har yanzu rundunar ba ta samu rahoton Hari ranar Lahadi ba, amma sun samu labarin Wanda aka yi ranar Lahadi.
Titin Kaduna zuwa Birnin Gwari yayi kaurin suna wajen tare mutane, kashe da yin garkuwa dasu.
Matafiya musamman a wannan hanya kan fada tarkon mahara da masu garkuwa da mutane da sai an biya kudin fansa kafin a sake su.
Haryanzu dai hare-haren mahara da masu garkuwa da mutane bai tsagaita ba a wadannan yankuna.