Mahara sun sace yayan gwamnan Bauchi

0

Mahara dauke da manyan bindigogi sun Yi garkuwa babban wan gwamnan Bauchi, Bala Mohammed.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun diran wa gidan Adamu Mohammed da aka fi sani da Yaya Adamu a daren ranar Laraba.

Adamu Mohammed sananne ne a garin Bauchi kuma gashi dan uwan gwamnan jihar Bala.

Maharan da suka afka gidan Adamu, sun bude wuta tun daga kofar shiga gidan ne har suka waske da shi.

Har yanzu ba a ji daga bakin wadanda suka sace Adamu mu ba tukunna.

Idan ba a manta ba, gwamna Bala na nan a killace a dalilin kamuwa da yayi da cutar coronavirus da yayi.

Share.

game da Author