Mahara sun kashe mutum daya, sun yi garkuwa da mutane shida a jihar Sokoto

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta bayyana cewa wasu mahara sun far wa kauyuka uku a karamar hukumar Shagari inda suka kashe mutum daya sannan suka yi garkuwa da mutane shida.

Kakakin rundunar Muhammed Sadiq ya sanar da haka wa manema labarai a garin Sokoto.

Sadiq yace wadannan mahara sun far wa kauyukan Gidan Shikkau, GidanTsamiya da Kajiji da misalin karfe uku na safiyar Litini.

Ya ce rundunar ta fara farautar wadannan mahara a duk inda su ke a kewayen wadannan kauyuka.

Wata majiya da baya so a fadi sunnan sa ya bayyana wa manema labarai cewa maharani sun shigo suna ta harbi ta ko ina inda a dalilin haka mutum daya ya mutu.

Majiyar y ace daga nan suka yi garkuwa da mutane shida.

Dan majalisar dokoki na jihar da ke wakiltan karamar hukumar Shagari a APC Maidawa Alhaji-Kajiji ya yi wa mutanen karamar hukumar ta’aziyar ‘wadan maharan aka rasa kuma ya jajanta wa ‘yan uwan wadanda aka sace.

Idan ba a manta ba a watan Yulin 2019 wasu mahara sun kai hari a wasu kauyukan dake karamar hukumar Goronyo inda suka kashe mutane 29.

Maharan sun banka wa shaguna wuta sannan sun sace shanu daga wadannan kauyuka.

Share.

game da Author