Gwamnatin jihar Barno za ta dauki daliban jami’ar Maiduguri (UNIMAD) 200 da suka kammala karatu a sashen koyon aikin malunta domin koyar da boko da Arabi a makarantun Allo da Islamiyya a jihar.
Gwamnati ta ce wadanan sabbin malamai za su karantar a makarantun Tsangaya da Islamiya a fadin jihar.
Manajan ilimi na asusun kula da al’amuran yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) Nasser Kaddoura ya sanar da haka a taron horas da wadannan malamai da aka dauka.
Kaddoura yace gwamnati ta yi haka ne domin karfafa gwiwowin yara wajen samun ilimin boko da na Islama sannan da rage yawan yaran dake gararamba a titunan jihar.
Ya ce burin gwamnati shine samar wa yara ilimin boko da na Islama inda bayan haka za su iya ci gaba da karatu nan gaba ko kuma su koyi sana’a.
“A dalilin haka UNICEF ta hada hannu da ma’aikatar ilimi da na harkokin addini domin ganin tabbatuwar hakan.
Bayan haka kakakin ma’aikatar harkokin addini Ummar Muhammed ya jinjina namijin kokarin da gwamnati ke yi a fannin ilimin jihar.
Muhammed yace gwamnati a shirye take domin ware isassun kudi domin ganin an zantar da wadannan ayyuka a jihar.
Daya daga cikin malaman da aka horas a taron Aminu Amatiao ya yi kira ga iyaye da su mara wa malaman baya wajen ganin ‘ya’yansu sun samu ilimi kamar yadda gwamnati ta shirya.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne ministan ilimi Adamu Adamu ya bayyana cewa gwamnati za ta ciyo bashin Naira biliyan 45 daga asusun ‘Global Partnership for Education (GEP)’ domin rage yawan yaran dake gararamba a kasar nan.