Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya ce gwamnati na kokarin kirkiro sabuwar shiri da zai sa ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya ci gaba da zama a cikin tsarin inshoran kiwon lafiya har sai sun shekara 70.
Ehanire ya fadi haka ne a taron inganta kiwon lafiyar tsoffi a kasar nan da aka yi a asibitin koyarwa na jami’ar Benin (UBTH).
Ya ce gwamnati ta hada hannu da hukumar fansho ta kasa, PTAD da NHIS domin ganin haka ya tabbata a kasar nan.
Idan ba a manta ba a watan Janairu 2020 hukumar inshorar kiwon lafiya ta kasa (NHIS) ta sanar cewa nan ba da dadewa ba hukumar za ta fara aiki da tsarin inshoran kiwon lafiya na bai daya wato ‘Health Insurance scheme under one roof’.
An kafa hukumar NHIS ne domin tallafa wa mutane wajen biyan kudin asibiti. Sai dai hakan da aka yi ba a kai ga samun nasara ba har yanzu domin mafi yawan mutane basu cikin tsarin kuma kadan dake cikin shirin suna matukar kokawa da rashin samun biyan bukata.
A dalilin haka ya sa NHIS ta kirkiro tsarin samar da tsarin inshoran kiwon lafiya a jihohi sannan ta kirkiro shiri na bai daya domin kula da aiyukkan da hukumomin inshorar ta tarayya da na jihohi ke yi a kasar nan.