Litan mai ya koma Naira 125 – Mele Kyari

0

Gwamnatin Najeriya ta sanar da rage farashin litan man fetur daga naira 145 zuwa naira 125.

Shugaban kamfanin mai na kasa, Mele Kyari ya bayyana cewa daga ranar 19 ga watan Maris za afar saida man Fetur nair 125 kowani Lita.

Idan ba a manta ba, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci gidajen man kasa da su rage farashin man fetur.

A sanarwan a wancan lokaci ba a fadi ko nawa bane za a siyar da lita daya na man fetur, shugaba Buhari ya ce ma’aikatar PPPRA zata fadi sabon farashin mai din.

Ministan Albarkatun man Fetur na kasa Timipre Sylva ne ya bayyana haka a takarda da aka fitar daga ofishin sa ranar Laraba.

Sylva ya ce hakan ya biyo bayan rugujewar farashin man fetur a kasuwannin duniya.

Mele Kyari ya kara da cewa a bisa matsalolin rugujewar tattalin arzikin kasashen duniya, gwamnati ta ga ya dace a rage kudin man fetur din saboda a rage wa mutane radadin zafin rashi da ake fama da shi.

Share.

game da Author