Kungiyar malaman jami’oin kasar nan sun fara yajin aiki na gama gari na makonni biyu a rashin kin biyan wasu daga cikin malaman jami’o’i albashi.
Shugaban kungiyar Biodun Ogunyemi ya bayyaa haka bayan ganawar gaggawa da kungiyar ta yi a garin Enugu.
Wannan yajin aiki na kwankwasa kyaure ne tukunna, idan gwamnati bata ce uffan ba za su fara yajin aikin gadan-gadan har sai an biya musu bukatunsu.
Daya daga cikin abin da suke kuka da shine dagewa da gwamnati tayi sai dole malamai sun yi rajista da shirin biyan albashi na IPPPIS kafina biya mutum albashi. Daya wa daga cikin malaman jami’oin ba su karbi albashin su ba saboda basu cikin shirin.