Kotun Daukaka Kara ta dakatar da dakatarwan da Kotun Abuja ta yi wa Oshiomhole

0

Kotun daukaka Kara ta dakatar da dakatan da kotun Abuja ta yi wa shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole.

Kotun ta yanke hukuncin a dakatar da wannan hukunci na kotun Abuja har sai an Saurari karar da Oshiomhole ya shigar a kotun daukaka Kara.

Hakan na nufin cewa, wancan hukuncin zai daina aiki yanzu sai kotun daukaka Kara ta zauna akan karar da aka shigar a gabanta.

Idan ba a manta ba kotun a Abuja ta dakatar da Oshiomhole daga ci gaba da bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar APC makonni biyu da suka gabata.

Wanda ya shigar da karar Lauya Afolabi ya ce babban hujjan su na shigar da Kara shine an dakatar da Oshiomhole daga jam’iyyar a mazabarsa da gundumar da.

Yace hakan ya tabbatar da Oshiomhole ba Dan jam’iyya bane a yanzu saboda haka bai cancanci ci gaba da zama a kujerar shugabancin jam’iyyar ba.

Sai dai ko a a wancan lokaci, wata kotun Mai karfin iko irin na Abuja, a Kano ta ya ke hukuncin wancakalar da dakatar da Oshiomhole da kotun Abuja ta yi.

Oshiomhole ya garzaya kotun daukaka Kara domin kalubalantar wannan dakatar da shi da kotu ta yi da kuma garkame ofishin jam’iyyar da hukumomin tsaro suka yi wai suna yin biyayyane ga hukuncin kotu.

A bisa wannan hukunci na kotu, Oshiomhole zai ci gaba da shugabancin jam’iyyar har sai an kammala shari’ a kotun daukaka Kara.

Shima jigon jam’iyyar APC Bola Tinubu ranar Lahadi ta bayyana goyon bayan sa ga shugaban jam’iyyar, Oshiomhole, Yana Mai cewa mutum Tara ne bai cika goma. Saboda haka laifukan Oshiomhole ba su Kai ga a ce wai sun shanye gwaninta da jajirce wa jam’iyyar da yayi a baya ba.

Share.

game da Author