Kotu ta umarci mahukunta su yardarwa Sanusi ya je duk inda yake so ban da Kano

0

Kotu a Abuja ta umarci mahunta a Najeriya da su kyale tsohon sarkin Kano Sanusi ya wataya yadda yake so a ko ina a fadin kasar nan ban da jihar Kano.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne ranar Juma’a bayan Lauyan Sanusi ya bukaci kotu ta ba tsohon sarki ‘yan cin watayawa kamar yadda doka ta bashi.

Haka kuma kotun ta bayar da kwana uku a bai wa wannan hukuncin da aka yanke ga wadanda aka kai karar su yi aiki da wannan hukunci da suka hada da Hukumar DSS, da sufeto janar na ‘yan sandan, ministan shari’a na Najeriya da kwamishinan shari’a na jihar Kano.

An dage zaman kotun sai ranar 26 ga wannan watan na Maris.

Idan ba manta ba tun bayan tsige sarki Sanusi da gwamnatin jihar Kano ta yi mutane ke ta tofa albarkacin bakin su game da haka.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya nada sarki Sanusi mukamai har guda biyu bayan an tsige shi sannan. Daya daga ciki shine shugabancin kwamitin gudanarwar Jami’ar jihar Kaduna.

A jihar Kano kuma, gwamna Ganduje ya nada Sarkin Bichi, Aminu Ado Bayero sabon sarkin Kano. Sannan aka nada Nasiru Ado Bayero Sarkin garn Bichi.

Share.

game da Author