Kotu ta hana belin masu adawa da Gwamnan Gombe bayan ta tura su kurkuku a ranar hutu

0

Mai Shari’a Abdullahi Abubakar da ke Kotun Yanki ta Pantami a Jihar Gombe, ya ki bayar da belin wasu matasan soshiyal midiya biyu, wadanda ya garkame a kurkuku a ranar hutu, saboda zargin “sun hada kai za su ci mutuncin gwamna.’

Matasan biyu masu adawa da Inuwa Yahaya, Gwamnan Gombe, wato Atiku Boza-boza da kuma Adamu Babale, dukkan su ‘yan jam’iyyar PDP ne. An tura su kurkuku bayan an tuhume su a ranar da gwamnatin jihar Gombe ta kebe ranar hutun alkalan jihar.

Tun a ranar Alhamis aka tura su kurkuku, bayan da aka gabatar da su, kuma a lokacin ba su da wani lauya wanda ya tsaya a kan shari’ar ta su.

Sai dai kuma a ranar Litin ko Talatar da ya kamata a maida su kotu, sai akalin ya rika yi kulli-kurciya da wani lauyan da suka samu, mai suna Habu Abdu. Haka Abdu din ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Gwamantin Gombe Ta Shiga Shari’ar Tsundun

A ranar Talaka sai aka yi jirwaye mai kama da wanka, inda mai shari’a ya sanar cewa gwamnatin jihar Gombe ta aiko wa kotun da wasika cewa ta shiga cikin shari’ar.

Ma’aikatar Shari’a ta Jiha ta ce za ta karbi gabatar da masu karar da kan ta daga hannun ‘yan sanda.

Kwamishinan Shari’a na Jihar Gombe, Zubairu Umar, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES da haka a ranar Talata.

Wannan karbar gabatar da shari’a kuwa ya saba daga matsayar da kakakin gwamnatin Gombe, Abdullahi Mislili ya fara shaida wa Premium Times bayan an tura sunkurkuku, cewa babu hannun Gwamna Yahaya a cikin lamarin.

“Umar ya ce akwai batu na tsaro a cikin sha’anin na su, Don haka ba mu son a rike batun ba kan yadda ya kamata a dauke shi ba.” Haka kwamishinan ya furta wa Premium Times, a lokacin da ya ke kokarin bayyana dalilin shigar gwamnatin jihar Gombe a cikin lamarin.

Ranar Litinin PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda wata kotu ta tura masu adawa da Gwamnan Gombe kurkuku a ranar hutu.

Mai Shari’a na Kotun Yanki (Area Court) a Gombe, ya tura wasu ‘yan siyasa masu adawa da Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe zuwa kurkuku.

Sai dai kuma abin da ya daure wa mutane kai shi ne yadda ‘yan sanda suka gurfanar da su a kotu, da kuma yadda alkalin ya yi zaman sauraren shari’ar ta su a ranar da aka ce kada kowace kotu ta yi aiki a Jihar Gombe.

‘Yan sanda sun kama wani tsohon Hadimin Tsohon Gwamna Ibrahim Dankwambo, mai suna Boza-boza, a bisa zargin ya ci mutuncin Gwamna Inuwa Yahaya.
Wannan kamu da aka yi wa Boza-boza tare da abokin sa Adamu Babale, ya sa Jihar Gombe ta shiga sahun jihohin da ake garkame masu adawa da gwamna a soshiyal midiya.

Watannin baya PREMIUM TIMES ta yi cikakken rahoton kan jihohin da gwamnonin su ba su da jimirin suka daga bakin masu adawa a soshiyal midiya.

Bayan an kama Boza-boza an kulle a Ofishin ‘Yan Sanda na Pantami, sai abokin sa mai suna Adamu Babale ya je belin sa. Maimakon a ba shi beli, sai shi ma aka damke shi.

‘Yan sanda sun zarge su da laifin “kokarin zagin wani mai suna Inuwa Yahaya.” Daga nan an daure da ankwa, aka tasa keyar su zuwa kotu.

Duk da cewa Kwamishinan Shari’a na Jihar Gombe, Mu’azu Pindiga ya bada hutu ga dukkan kotina da alkalan kasar, hakan bai hana alkalin fitowa kotu ba, domin ya yi hukunci a kan batun. Ya kuma tura su kurkuku take.

Kakakin Gwamnan Gombe Abdullahi Misili_ya nesanta Gwamna Yahaya daga kamun da aka yi musu.

Ana tuhumar Boza-boza saboda ya kira Inuwa “Shugaban marasa cika alkawari.”

Share.

game da Author