Kotu a Kano ta yanke cewa har yanzu Oshiomhole ne shugaban APC

0

Idan ba a manta ba Kotu a Abuja ta dakatar da shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole daga ci gaba da nuna kansa a matsayin shugaban Jam’iyyar APC na Kasa.

Kotun ta ce a dalilin dakatar da shi da jam’iyyar ta yi tun daga mazabar sa, ci gaba da nuna kansa a matsayin shugaban jam’iyyar ya haramta masa.

Sai dai kuma wata babban kotu a jihar Kano, ta sauya wannan hukunci da aka zartar a kotun Abuja inda ta zartar cewa har yanzu Oshiomhole ne shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Kotun ta ce a yi watsi da wancan hukunci da Kotun Abuja ta yanke.

Bayan haka Oshiomhole ya bayyana cewa gwamnan jihar Edo Obaseki ne yake yi masa zagon Kasa. Ya ce shine yake kulla masa wannan kamayamaya don yaga bayan sa.

Idan ba a manta gwamnan Edo da shugaban APC, Oshiomhole tuni suka raba jiha inda kowa yake yi kowa sari ka noke.

Abin ya fito fili kara a ‘yan kwanakin nan inda mazabar Oshiomhole ta dakatar da shi daga jam’iyyar.

Hakan ne ya sa wasu suka garzaya kotu domin ta dakatar da shi daga ci gaba da nuna kansa shugaban jam’iyyar.

Wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar APC sun nuna jin dadin su kan da dakatar da Oshiomhole da kotu tayi suna masu cewa dama shine ya gurgunta jam’iyyar ya sa ba ta yi nasara yadda ta so ba a zaben 2019.

Sai dai kuma wasu da dama na ganin ana yi wa Oshiomhole wannan zagon kasa ne saboda katangar da ya gina tsakanin wasu dake ganin su shafaffu da mai ne a jam’iyyar da ita kanta uwar jam’iyyar.

Share.

game da Author