Komawa ga Allah shine mafita a gare mu – sakon Trump

0

Shugaban kasar Amurka Donald Trump yayi kira ga ‘yan kasan su koma ga Allah, kowa ya daga hannu ya roki Allah musamman a yau ranar Lahadi da ranar Ibada ne.

“Da ya ke mu Amurkawa a tsawon tarihi mukan yi tawassuli ga Ubangiji, a duk lokacin da mu ka samu kan mu cikin irin wannan mawuyacin halin, ina mai sanar da cewa ranar Lahadi 15 Ga Maris ta kasance Ranar Addu’ar Kasa Baki Daya. Za mu yi addu’o’in ne domin neman tsari da kariya daga Ubangiji.”

“A kowane hali ko yanayi ka tsinci kan ka, ina kira da ka maida himma wajen dukufa da yin addu’a tare da mika wuya da imani ga Ubangiji. Idan muka hada hannu, sai mu tsira tare sannan mu kubuta daga wannan annoba.”

Trump bashi da coronavirus

Bayan gwajin shugaban kasar Amurka Donald Trump da aka yi domin samun tabbacin ko yana dauke da cutar coronavirus, an gano cewa ba shi da shi.

Mutane a kasar Amurka sun nemi shugaba Trump yayi gwajin cutar bayan ganawa da shugaban kasan Brazil da yayi da ake zaton ya kamu da cutar.

Trump ya bayyana cewa shi ba zai yi gwajin ba da farko sai kuma daga baya ya amince zai yi.

Likitocin sa sun tabbatar masa cewa ba ya dauke da wannan cuta.

Har yanzu dai masana kimiyya na can suna ci gaba da aiki tukuru domin kirkiro maganin wannan cuta da ta karade duniya.

Share.

game da Author