KISAN KIYASHIN KADUNA: Ku yi hakuri da gazawar mu – El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya roki mutanen jihar Kaduna da su yi hakuri su yafe wa gwamnati a dalilin rashin iya samar musu da tsaro a fadin jihar.

Idan ba a manta ba mahara sun kashe sama da mutane 50 a kauyuka shida dake kananan hukumomin Giwa, Birnin Gwari da Igabi ranar Lahadi a jihar.

Ire-iren wannan hare-hare ya kazanta a yankin Arewacin kasar nan.

A ziyarar jaje da ya kai wadannan kauyuka, gwamna El-Rufai ya nuna takaicin sa game da abinda ya faru sannan ya ce kwazon gwamnati ya gajarta matuka wajen samar wa mutane tsaro a kasar nan.

” A matsayina na shugaban jama’a da ke jagorantan su, samar da tsaro shine abinda ya kamata in fi maida hankali a kai domin ya rataya a kai na ne da sauran ‘yan uwana. Na zo gaban ku domin in roke ku gafara a bisa gazawa ta.

” Gwamnati na kokarin ganin an gama da wadannan mahara, amma kuma idan an toshe nan sai can ya balle. Yankin na da girman gaske da za a ce wai an iya tunkarar sa lokaci daya. Amma muna kokarin ganin an rage kai ire-iren wannan hare-hare. Muna rokonku gafara, ku yafe mana.”

” A jihar Kaduna ba za mu daga kafa wa kowanne dan bindiga ba, ba za mu basu lamuni ba kuma ba za mu tattauna da su ba. Hakkin mu ne mu kakkabe su duka, mu aika da su lahira, jami’an tsaro za su rika bin su har inda suke suna gamawa da su har sai mun kakkabe su tas.”
 

Share.

game da Author