KISAN KIYASHIN KADUNA: Ko gwamnonin Arewa su farka daga barci ko kuma a wayi gari babu Arewa – Shehu Sani

0

Sanata Shehu Sani ya yi kira ga gwamnonin Arewa da lallai fa lokaci yayi da su farka daga barci, su san yadda za a kawo karshen hare-haren yan bindiga a yankin ko kuma a wayi gari wata ra na babu ma Arewan.

Sanata Sani ya bayyana cewa ‘yan bindiga na cin karen su ba babbaka a yankin Arewa, kullum maimakon a samu sauki abu sai gaba-gaba yake yi.

” Musulmai da ake kashewa bai zama abin tashin hankali ba saboda shugabannin su ba su sun su yi maganan da zai bata wa gwamnati rai, su ko kiristoci, a kullum suna fitowa su nuna damuwar su da rashin jin dadin su game da abinda yake faruwa na kashe-kashen mutane da ake yi.

” Gaba daya gwamnonin Arewa suna tsoron su tunkari gwamnatin tarayya su gaya mata gaskiya, alhali a nan ana ta kashe mutanen su ana yin garkuwa da su.

” Matsalar rashin tsaro a Arewa ya na samun mazauni ne a dalilin munafince-munafincen da shugabannin yankin ke yi na kin fadi wa gwamnati gaskiyar matsalolin da ake fama dasu. Sai a rika yi kamar komai lau.

” Idan ana kashe mutanen mu, ana sace su, kuma muka fito muka yi magana, sai gwamnati da ‘yan kanzagin ta su fito suna cewa wai siyasa ce, ba gaskiya ba.

” Matsalar tsaro a Arewa ya zama annoba a yankin da kasa baki daya kuma ya zama abin tashin hankali ya yankin Afrika ta Yamma. Dole gwamnoni su hadu su samar da wani runduna, ko tsari don samar wa mutanen yankin tsaro wallahi, ko kuma duk mu zama abin tausayi.

Yadda ‘Yan bindiga suka bindige mutane 50 a Kaduna

Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu gungun ‘yan bindiga sun kai farmaki ya yanku hudu da ke karkashin Karamar Hukumar Igabi, har suka kashe mutane 50.

Sun kai wannan mummunan farmakin ne a kauyukan Kerewa, Zareyawa da Marina, dukkan su a cikin Mazabar Kerawa.

Kafafen yada labarai sun tabbatar da cewa an kai farmakin ne wajen karfe 6 na safiyar Lahadi, daidai lokacin da ba a dade da gama sallar asubahi ba.

An ce maharan ba su bar babba ko yaro ba, hatta jira-jirai sabuwar haihuwa da almajirai sai da suka kashe.

Mazauna kauyukan sun rika tserewa, yayin da ake harbin su. An kuma banka wa gidaje masu tarin yawa wuta, kuma an saci kayan abinci.

Kansilan Mazabar Ketawa, Dayyabu Kerawa ya shaida cewa mutum 51 aka kashe, kuma babu wanda ya san za su kai hare-haren, sai dai kawai aka gan su.

An kasa samun lambar kakakin yada labarai na ‘yan sandan Jihar Kaduna. Haka shi ma Kwamishinan Tsaron Cikin Gida, Samuel Aruwan, ba a samu lambar sa ba.

Amma daga baya kakakin ‘yan sanda ya tabbatar wa manema labarai cewa an kai harin.

Cikin 2019 garuruwan cikin Kananan Hukumomin Kajuru, Giwa da Igabi sun sha fama fa hare-haren ‘yan bindiga.

Sun taba sanar da mazauna wasu kauyukan Igabi cewa su tashi ko su far musu. Hakan ta sa tilas dubban jama’a suka yi Laura zuwa Birnin Yero, inda suka yi mafaka cikin ajujuwan firamaren garin.

Share.

game da Author