Kasashe 20 da coronavirus bai afka musu ba

0

Sakamakon bincike ya nuna cewa akwai kasashe 20 da har yanzu ba su kamu da cutar coronavirus ba.

Sakamakon ya nuna cewa duk da haka wadannan kasashe sun dauki tsauraran matakai domin hana cutar shigowa kasashen su.

Wadannan kasashe na Nahiyoyin duniya bakwai da; Asia, Afrika, Europe, Australia, Amurka ta Arewa, Amurka ta Kadu da Antarctica.

NAHIYAR AFRIKA

Akwai kasashe 54 a Nahiyar Afrika inda daga ciki 46 sun kamu da coronavirus sannan cutar bata bullo ba a kasashe takwas ba.

Botswana, Burundi, Lesotho, Malawi, Sao Tome and Principe, Sierra Leone da Sudan ta Kudu na daga cikin kasashen da cutar bata Kai gare su ba sannan gwamnatin kasashen sun dauki tsauraran matakai domin kada cutar ya diran musu.

A kasar Botswana Shugaban kasan Mokgwetsi Lasisi ya kafa dokar hana shiga da fita a kasar.

Ya ce ya yi haka ne bisa ga shawarwarin da masana kimiya dake kasar suka bashi.

Burundi Ta hana tashi da saukan jiragen sama sannan Lesotho ta kafa dokar hana walwala wanda zai fara aiki ranar 29 ga watan Maris zuwa ranar 21 ga watan Afrilu.

Malawi ta hana taron mutane sama da 100 da sauran su.

Sao Tome da Principe sun kafa dokar tabaci a fannin kiwon lafiyar su a ranar 17 ga watan Maris.

Sierra Leone ta kafa dokar tabaci a fannin kiwon lafiya ranar 24 ga watan maris sannan ta hana duk jami’an gwamnati fita zuwa kasashen waje tare da hana taro mutane sama da 100 a wuri daya.

Sudan ta Kudu ta kafa dokar hana walwala gaba daya a kasar.

YANKIN ASIA

Har yanzu cutar ba ta fada Korea ta Arewa, Tajikistan, Turkmenistan, da Yemen

EUROPE

Duk kasashen dake wannan Nahiya sun kamu da coronavirus sannan sama da mutane 247,667 sun kamu da cutar 13,895 sun mutu.

AMURKA

Ita ma ta kamu da cutar duka.

OCEANIA

Akwai kasashe 10 a wannan Nahiya da basu kamu da cutar ba.

Amma Kasar Australia ta fi fama da cutar a cikin yawan kasashen da suka kamu da ita a wannan Nahiya.

Mutane 3166 suka kamu da cutar a Australia. Ga kasashen Solomon Islands, Vanuatu, Samao, Kribati, Micronesia, Tonga, Marshall Islands, Palau, Tovalu da Naura.

Share.

game da Author