KARYA DOKA: Gwamnatin Kaduna ta cafke limamai biyu da suka gudanar da Sallar Juma’a

0

Gwamnatin jihar Kaduna ta cafke wasu malamai biyu da aka samu suna karya dokar jihar na hana taro da ya hada da salloli a masallatai.

Wadannan malamai sun bijirewa dokar jihar, suka gudanar da sallar Juma’a a masallatan su.

Idan ba a manta ba gwamnatin Kaduna ta saka dokar ta baci a jihar da ya hada da dakatar da yin salloli gaba daya harda sallar Juma’a.

Hakan kuma an rufe kasuwanni, da wuraren shakatawa domin kada a yada cutar a jihar.

A wata sanarwa da kwamishinan tsaro
da harkokin cikin gida na jihar Samuel
Aruwan ya fitar, an cafke Malam Aminu Umar Usman Unguwan Kanawa da Malam Umar Shangei da yayi sallan Juma’a a Malali.

Aruwan ya ce gwamnati za ta za a gurfanar da wadannan malamai a kotu nan ba da dadewa ba.

Bayan haka kuma gwamnati ta yabawa sauran manyan malamai da suka bi wannan umarnin gwamnati suka dakatar da yin taruka a masallatan su.

Wannan doka da gwamnati ta saka ya biyo bayan barkewar cutar coronavirus da ya karade duniya ne.

Duk da dai ba a samu wanda ya kamu da cutar a jihar Kaduna ba, gwamnatin jihar karkashin Nasir El-Rufai ta maida hankali wajen ganin ba ayi da na sani ba.

Hanya mafi sauki shine a daina cudanya da mutane da sannan a rika zama wuri daya.

Share.

game da Author