JIGAWA: Wani hasalalle ya yi wa Gwamna Badaru tsiwa a cikin taro

0

Wani hasallale ya shiga hancin Gwamna Badaru Abubakar da kudundune a wurin taro, ya nuna wa gwamnan fushin yadda ya kasa kammala aikin asibitin Birnin Kudu da titin hanyar Birnin Kudu, cikin Jihar Jigawa.

Al’amarin ya faru lokacin da Badaru ke ta kokarin lissafa ayyukan da Gwamnatin Tarayya ta yi a jihar. Sai can daga nesa aka ji wani da ba a gane ko wane ba, ya katse gwamnan, ya na cewa: “Ka yi mana alkawarin aikin titin Birnin Kudu da asibitin Birnin Kudu. Amma har yau babu abin da aka yi a karkashin ka.”

Dan Majalisar Tarayya Magaji Aliyu ne ya yi birin raba tallafin karatu ga dalibai 5000 a Birnin Kudu, inda Badaru ya halarta.

Mafusacin dai na magana ce a kan aikin asibitin Birnin Kudu da aka fara tun a zamanin gwamnatin da ta shude, amma tuni aikin ya tsaya cak a zamanin wannan gwamnati.

Cikin fushi shi kuma gwamna Badaru ya maida masa amsa da cewa: “Ka taba ganin inda na yi alkawarin yin aiki amma na kasa kammalawa? To ni zan cika dukkan alkawurran da na dauka.”

Laifin Dan Kwangila Ne -Badaru
Gwamna Badaru ya dora laifin rashin kammala aikin a kan dan kwangila, kamar yadda ya furta.

“Wannan dan kwangilar raggo ne. Mun shi kudi ya karasa amma har yau bai kasara ba. Gwamnatin da ta gabata ce ta bayar da kwangilar, amma kuma ni na ci gaba da aikin.

“Saboda ragwanci da lalacin dan kwangilar, sai da ma ta kai an yi tunanin kwacewa daga hannun sa, amma sai muka ga yin hakan zai dauki tsawon lokaci ana tabka shari’a a kotu. Sannan kuma lokacin da za a bata din zai iya amfani da shi ya kammala aikin baki daya.”

Badaru ya ce zai cika alkawarin kammala aikin kafin nan da karshen wannan shekara.

“Ina tabbatar muku cewa zan kammala aikin kuma a kaddamar da shi, duk a cikin wannan shekarar.”

Share.

game da Author