A ranar Alhamis ne gwamnatin Jigawa ta sanar cewa ta datse iyakokinta domin hana mutane shigowa daga jihohin Bauchi da sauran jihohin dake makwabtaka da ita.
Gwamnati ta yi haka ne domin hana yaduwar cutar musamman yadda cutar ta bayyana a jihar Bauchi.
Kwamishinan lafiya na jihar Abba Zakari ya fadi haka kuma yace dokar zata fara aiki ranar Juma’a 27 ga watan Maris.
Zakari ya ce gwamnati ta tattauna da kungiyar motocin haya na jihar (NURTW) domin ganin mutane sun bi wannan doka.
Ya kuma ce gwamnati ta datse titunan Kano, Katsina da Yobe da matafiya ke bi su shigo jihar Jigawa.
Zakari ya ce gwamnati ta zuba ‘yan sanda a jihar domin ganin mutane sun bi wannan doka da gwamnati ta saka.
Gwamnati ta kuma hana taron mutane sama da mutum 20 a jihar.
“Gwamnati baza ta yi kasa-kasa ba wajen ganin ta kare duk mutanen jihar daga kamuwa da cutar”.
Coronavirus wace ta samo asali daga kasa Chana ta yi ajalin mutane da dama a duniya sannan har yanzu cutar ta ci gaba da yaduwa a kasashen duniya.
A Najeriya mutane 65 sun kamu da cutar uku sun warke sannan daya ya mutu.
Hanyoyi 10 da za a kiyaye domin kare kai daga CORONAVIRUS
1 – A rika Wanke hannuwa da sabulu a duk lokacin da aka dan wataya ko kuma aka yi tabe-taben abubuwa. Ko bako Kayi ka bashi dama ya wanke hannu kafin ku fara mu’amala.
2 – Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da gefen Hannu amma ba da tafin hannu ba. Idan kun shafi bakunan ku toh, ku wanke hannu maza-maza.
3 – A daina taba idanuwa da hannaye ko kuma hanci da baki. Ka du rika yawan shafa fuskokinku da hannaye. Idana an yi haka a gaggauta wanke hannaye.
4 – A nisanci duk wani da bashi da lafiya, musamman mai yin Mura da tari. Ko zazzabi ne yake yi a nisanta da shi sannan a bashi magani da wuri. Idan abin ya faskara a gaggauta kaishi asibiti domin a duba shi.
5 – A kula da yara sannan a rika tsaftace muhalli.
6 – A rika gaisawa da juna nesa-nesa
7 – Idan kayi bako daga kasar waje, kada a kusance shi koda dan uwana ne sai ya killace kan sa na tsawon makonni biyu.
8 – A rika Karantar da yara yadda za su kiyaye koda an aike su a waje.
9 – A yawaita cin abinci masu gina jiki, shan ruwa da motsa jiki.
10 – A yawaita yin addu’a da sadaka.
Discussion about this post