JAWABIN SHUGABAN KASA: Ba a iya wa mutum, Daga Hassan Lawal

0

Wani abu da ya ke bani mamaki da ban takaici a lokutta da yawa shine yadda ba a iya wa mutane. A duk lokacin da ka ce za kayi wani abu sai ka ji wasu sun kushe ko da ka yi don su ne.

A jawabin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da yayi wa ‘yan Najeriya ranar Lahadi ya bayyana cewa za a garkame jihohin Legas, Ogun da Abuja. Fadin haka ke da wuya sai wasu suka fara sukar wannan doka da ya saka cewa ba abi dokar kasa ba.

Suka fara kawo kabli-da ba adi akai cewa ai kamata yayi ya saka dokar a duk kasa ne ba jihohi biyu ba da babban birnin tarayya.

Amma kuma da dama daga cikin ‘yan kasa sun yi ta kushe shugaban kasa cewa bai kyauta ba da ya bari ana ta walwala a jihohin da aka tabbatar da cutar ta kamu.

Tun kafin shugaba Buhari ya bayyana matsayin gwamnati, jihohi suka saka dokar hana walwala a jihohin su. Hakan ya sa dole aka garkame wadannan jihohi har sai lokacin da aka ga an samu sauki.

Amma fadin garkame jihohin Ogun da Legas da babban birnin tarayya ya sa kuma wasu suna cewa da ba haka aka yi ba.

Kai mutum ba a iya masa.

A Kafofin yada labarai na zamani, da sada zumunta, Soshiyal Midiya mutane sun rika kokawa cewa rashin rufe filayen jiragen saman Najeriya ne ya sa coronavirus din ya fado kasar. Amma Kuma daukan mataki domin dakile yaduwar wannan cuta ya sa wasu na ganin a nan ne ba a yi daidai ba don suna da abin cewa.

Kasashe da dama sun garkame kasashen su duk sun saka wadannan dokoki amma wasu na ganin ba a bi doka ba wajen saka dokar garkame jihiohin Legas da Ogun da kuma babban birnin tarayya.

Idan kuma abin ya karade kasa, sai ace gwamnati bata garkame wuraren da ya kamata ba shine ya sa ba a iya dakile yaduwar cutar ba.

Kai Mutum Ba a iya masa.

Me ake so kuma gwamnati ta yi bayan kalaman da Buhari yayi da irin kokarin da take yi?

Ni dai a nawa ganin duk da cewa akwai gazawar gwamnati a wasu fannonin, idan ta yi abin da ya kamata bai kamata ace kuma za a kushe ta ba.

A duk duniya kowa ya sani cewa wannan annoba abar yin kaffa-kaffa da ne. Mutane sai mutuwa suke yi a kasashen da suka fi mu ci gaba a sanadiyyar cutar. Babban abin daHukumar Lafiya ta duniya ta fadi ya fi dacewa a yi shine a guje wa cudanya da juna.

A rage zirga-zirga sannan a rika zama wuri daya.

A Najeriya Legas da Abuja ne wuraren da aka suka fi samun yawan wadanda suka kamu da cutar. Kun ga ko dole ne a dakatar da zirga-zirga da cudanya da jama’a domin talakawa.

Komai aka yi hakuri a aka yi masa addu’a mai wucewa ne.

Share.

game da Author