Shugaban Kasa Mohammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnati ta saka dokar hana shiga da fita garin Abuja, Jihar Legas da jihar Ogun.
Buhari ya ce dole a dakatar da shiga wadannan jihohi da babban Birnin tarayya domin a iya dakile yaduwar cutar coronavirus a jihohin da Abuja.
Ya ce a wadannan lokaci babu wanda za a bari ya shiga wannan garuruwa ta sama ko kasa.
Bayan haka kuma za a biya masu karbar kudaden tallafi na tireda moni da kudin tallafi na manoma da kuma kudaden da ake ba gajiyayyu.
Bayan haka ya kara da cewa duk masu harkoki da ya shafi al’umma, kamar jigilar mai, abinci da harkarvwutan lantarki duk za su ci gaba da aiki.
Shugaba Buhari ya ce gwamnati za ta ci gaba da mara wa hukumar NCDC da ma’aikatar kiwon lafiya baya don ganin an kai ga yin nasara a wannan yaki da aka sa a gaba na dakile yaduwar cutar.
Daga karshe ya roki mutane su bi wannan doka sau da kafa domin ya zama dole a hada hannu domin a yi nasara gaba daya.
Akwai akalla mutane 97 davsuka kamu da cutar a Najeriya.
Shugaban ma’aikatan fadan shugaban kasa, Abba Kyari, gwamnonin Bauchi da Kaduna suna daga cikin jigajigan gwamnati da suka kamu da cutar.
Discussion about this post