Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa sama da mutane 400 sun kamu da cutar coronavirus wadda daga cikin su 41 sun warke a Afrika.
Hakan ya sa kasashen Nahiyar rufe tashohin jiragen sama da ruwa da iyakokin kasashen su domin hana yaduwar cutar.
Cutar ta yi wa kasar Masar kamun farad daya inda a kasar mutane sama da 150 suka kamu da cutar kuma mutum biyu sun rasu.
A yanzu dai kasar Masar ta hana jiragen sama sauka da tashi daga a kasar daga ranar Alhamis kuma gwamnati ta rufe duk makarantu da jami’o’I a kasar na tsawon makonni biyu.
Ga yadda yake a Afrika zuwa yanzu
Algeria 60; 5 sun mutu; 10 sun warke
Benin 1
Burkina Faso 15
Cameroon 5
Central African Republic 1
Republic of Congo 1
Cote D’Ivoire 5
Democratic Republic of Congo 3
Egypt 164; 6 sun mutu; 26 sun warke
Equatorial Guinea 1
Swaziland 1
Ethiopia 6
Gabon 1
Ghana 7
Guinea 1
Kenya 4
Liberia 2
Morocco 41; 1 ya mutu ; 1 ya warke
Mauritania 1
Namibia 2
Nigeria 8; 1 ya warke
Rwanda 7
Sudan 1 ya mutu
Senegal 26; 2 sun warke
Somalia 1
Seychelles 4
Tunisia 24; 1 ya mutu
Tanzania 1
Togo 1
South Africa 85
Discussion about this post