‘Ya’yan marigayi Ado Bayero biyu sun dare kujerun sarautan masarautu biyu a Kano.
Ciroman Kano, Nasiru Ado Bayero ya dare kujerar sarautar masarautar Bichi.
Hakan ya biyo bayan nada wansa Aminu Ado Bayero sabon Sarkin Kano da gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje yayi.
Idan ba a manta ba Gwamnatin jihar Kano ta tsige sarkin Kano Muhammadu Sanusi daga kujerar sarautar Kano.
Sakataren gwamnatin jihar Usman Alhaji ya sanar da tsige Sarkin Sanusi a jawabin da yayi bayan ganawa da majalisar zartaswar jihar tayi ranar Litinin.
Alhaji ya ce majalisar ta amince da tsige sarki Sanusi daga kujerar sarautar masarautar Kano daga yau Litini.
Idan ba a manta tun bayan zaben 2019 zaman aminci ya karae tsakanin gwamnan jihar Kano da Abdullahi Ganduje da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
Gwamnan Kano Ganduje ya zargi Sarki Sanusi da kin mara masa baya a lokacin zaben sa a karo na biyu a 2019.
Rantsar da gwamna Ganduje ke da wuya sai ya fara da kirkiro sabbin masarautu a jihar da ke daidai da masarautar Kano. Dama kuma Jiahr Kano ita ce jiha daya tilo a Arewacin Njeriya dake Sarki mai cikakken iko daya.
Ganduje ya kirkiro sabbin Masarautu har hudu.
Masarautun sune,Rano, Gaya, Bichi da Karaye.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Muhammad Garba, ne ya sanar da haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai a wancan lokaci in ya ce hakan ya biyo bayan rusa masarautun ne da kotu tayi a bisa dalilin cewa ba a kirkiro su bisa ka’ida ba.
” Ina so ku sani cewa, wasu masarautun da aka kirkkiro sun fi masarautar Kano asali da dadadden tarihi. Sun kafu tun kafin masarautar Kano. Wannan yana daga cikin dalilan da ya sa muke so mu dawo wa wadannan masarautu ikon su da martaba.
” An taba kokarin kirkiro irin wadannan masarautu amma ba su dore ba, a yanzu gwamnatin Ganduje na so ta ga hakan ya tabbata sannan sun tsayu gidigam.
Garba ya ce bayan haka anyi gyara ga dokar d masarautun Kano domin kawo ci gaba a jihar ne sannan ya yi kira ga majalisar dokokin jihar da su gaggauta kammala aiki a kai domin ba gwamnati damar kirkiro wadannan masarautu.
Masarautun da majalisa ta amince da su sun hada da Masarautar Rano, Gaya, Bichi da Karaye