Babban Mai Shari’a a Kotun Koli, Centus Nweza, ya furta cewa hukuncin da alkalan Kotun Koli shida suka yanke, wanda suka jaddada kujerar gwamnan Imo ga Hope Uzodinma na APC, zai dade ya na damun martabar Najeriya.
Nweze wanda shi ne alkalin da bai amince da saran ba, ya ce danyen hukuncin ya zama wata bakar fatalwa, wadda za a dauki tsawon lokaci ta na damun Najeriya a shari’ance da siyasance da kuma kima da martabar kasar.
Haka ya furta a lokacin da ya ke bayanin cewa Emeka Ihedioha na PDP ne ya kamata ya zama gwamna.
Ranar Talata ne alkalan Kotun Koli da suka hada da Cif Jojin Najeriya Tanko Muhammad, Olukayode Ariwoola, Sylvester Ngwuta, Kudirat Kekere-Ekun, Amina Augie da Uwani Abba Aji suka ce babu wani dalili da har Ihedioha zai nemi a maida masa kujerar sa da kotun koli din ta kwace ta bai wa Uzodinma.
Sun ce alkalami ya rigaya ya bushe, Kotun Koli ba za ta iya soke wata shari’a da ta rigaya ta yanke ba.
Amma shi Nweze cewa ya yi Kotun Koli na iya warware wani hukunci da ta yanke, musamman idan aka tabbatar da karara an yi kuskure ko rashin aldaci a wurin yanke hukuncin.
Ya ce maganar gaskiya Uzodimma ba halastaccen wanda ya ci zabe ba ne, don haka shi dai a matsayin sa na alkalin Kotun Koli, bai amince Uzodinma ya ci zabe ba.
“ Emeka Ihedioka na PDP shi ne halastaccen gwamna. Don haka ina kira ga Hukumar Zabe ta INEC ta gaggauta damka sakamakon shaidar cin zabe ga Ihedioka.
Kotun Koli dai ta bai wa Uzodinma kujeraar gwamnan, duk kuwa da cewa shi ya zo na hudu, kuma alkaluman kuri’un da Kotun Koli ta kara masa, sun zarce wadanda aka INEC ta tantance a ranar zabe da kusan kuri’u 100,000.
Ita kan ta INEC ta ce ta karbi hukuncin Kotun Koli, amma ba ta yarda cewa Uzodinma ne ya yi nasara ba. INEC ta ce Ihedioha ne ya lashe zaben.