Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya bayyana cewa lallai ba shi bane Bala Mohammed din dake cikin jerin sunayen masu mallakin kamfanin Adda da gwamnatin sa ta dankara wa kwangilar siyan motocin naira biliyan 3.6.
Idan ba a manta ba wani binciken kwa-kwaf da PREMIUM TIMES ta yi ta gano cewa har yanzu dai a bayanan dake kasa sannan ke a hukumar rajistan kamfanoni ta kasa CAC sunan gwamna Bala na jerin sunayen masu mallakin wannan kamfani.
PREMIUM TIMES ta gano cewa ko a wadannan motocin da za a siyo sai da aka kara kudaden farashin su fiye da yadda aka saka tun a farko za a siya.
Bayan kauce wa ka’idojin da doka ta gindaya na yadda za abi da sai dole an tallata ire-iren manyan kwangiloli irin haka da tsohon kwamishinan kudin jihar Nura Soro ya ja kunnen gwamnati akai duk da kokarin saka wasu kamfanoni biyu a cikin bayanan takardun tallata gwangilar wai suma sun taya, gwamnati ta yi gaban kanta ne kawai ta amince wa wadda take so.
Haka dai daga baya a dalilin cakwakiyar da ta kanannade wannan kwangila kawai Soro ya hakura da kujerar kwamishinan da yake kai.
Sannan ko a cikin kasafin kudin jihar na 2019, naira biliyan 1 ne kacal aka amince a siyo motocin da su.
Sai dai kuma a martani da gwamnan ya bada ta hannun kakakin sa, Mukhtar Gidado ya karyata wannan rahota, cewa babu ruwan sa da wannan kamfani cewa wannan suna Bala Abdulkadir Mohammed wani ne can daban ba shi ba.
Gidado ya kara da cewa duk hanyar da doka ta gindaya abi wajen bada kwangila a gwamnati gwamna Bala ya bi.
” Ba a bada wannan kwangila ba sai da aka tabbatar cewa an bi yadda doka ta gindaya. Saboda haka bamu shakkar komai. Haka kuma ma, sai da majalisar jihar ta zauna akai kuma ta amince da shi.
Sai dai kuma a binciken da PREMIUM TIMES ta yi bata ga inda aka saka wannan kwangila a kasafin kudin 2020 da majalisar jihar ta amince da ba kamar yadda Gidado ya yi korafi akai.
Kuma shi wannan Bala Abdulkadir Mohammed ba a bayyana shi ba ko shi wanene ba, sai adireshin kamfanin na nan a inda yake, wato gidan mahaifin gwamna Bala, da har yanzu ‘yan uwansa ne ke zaune a ciki.
Kamfanin Adda
Bincike ya nuna cewa ita dai wannan kamfani an kafa ta ne tun a shekarar 1996 da hannun jari na naira 500,000, Sannan da masu hannun jari hudu.
Abdullahi Salihu Bawa ne ke da kaso mafi tsoka a jarin kamfanin na naira 200,000, sannan gwamna Bala da wasu mutane biyu na da hannun jarin naira 100,000 kowannen su.
Gwamna Bala yayi amfani da adireshin gida mai lamba 227, Titin Gombe a takardun yin rajistan wannan kamfani.
A binciken da PREMIUM TIMES ta yi game da wannan gida ta gano cewa wannan gida na mahaifin gwamna Bala, Sarki Duguri ne. Yanzu wasu ‘yan uwansa ke zama a gidan sai kuma idan wansa ya zo Bauchi Sallah, da yake shine yake rike da sarautar mahaifin su Sarki Duguri.
Bincike bai nuna mana ko waye Abdullahi Bawa ba a Bauchi domin kamfanin bata da shafi a yanar gizo da za a iya dubawa don sanin ko wacce irin kamfanine da wadanda suke da mallaki, da irin ayyukan ta zuwa yanzu.
Bugu da kari, bincike ya nuna cewa kamfanin ta sake nada gwamna Bala a matsayin darekta a wannan kamfani a 2006 a hukumar CAC
Amma kuma dukka takardun da aka faffalle, aka dudduba, aka bincika, aka bi layi-layi daki-daki ba a ga inda gwamna Bala yayi sallama da wannan kamfani ba.
Sai dai ma ganowa da aka yi a takardun bayanai na kamfanin daga 2006 – 2018 cewa gwamna Bala yana nan daram a matsayin darekta a wannan kamfani, har a lokacin da yake ministan Abuja, da haka ma karya doka ce.
A haka ne kuma, a daidai lokacin da za a ba wannan kamfani kwangilar, sai kamfanin ta sanar wa CAC a watan Agustan 2019 nadin wani amini kuma makusancin Bala, mai suan Abdullahi Yari a matsayin Sakataren Kamfanin.
READ: EXCLUSIVE: Bauchi Gov. Bala Mohammed awards N3.6 billion contract to own company