Gwamnatin Jihar Kano ta hana harmutsa fasinjoji dankam cikin manyan motoci ana shiga da su Kano, saboda gudun fantsamar kamuwa da Coronavirus.
Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai Muhammad Garba ya saw a hannu, ranar Talata, ta bayana cewa sai wadanda ke gudanar da ayyukan musamman ne kadai aka dauke wa umarnin tsayawa gidajen su.
Kwamishinan ya kara bayyana cewa majalisa ta amince da matakan da aka dauka domin hana barkewar yaduwar cutar Coronavirus a Kano, birni na biyun yawan jama’a a Najeriya.
Hana Bas-bas makare mota da fasinjoji
Garba ya ce har yau dai ba a samu ko da rahoton mutum daya da ya kamu da cutar a Kano gaba dayan jihar ba. amma dai ana daukar matakan ne domin hana barkewar annoba.
Don haka an hana shiga Kano da lodin fasinjoji dankam a cikin manyan motoci.
Ya ce akwai hadari sosai a irin lodin da ake yi wa manyan motocin bas-bas, inda ake loda musu jama’a a cunkushe.
“Gwamnatin Jihar na aiki ba dare ba rana domin tabbatar da cewa wannan cuta ta Coronavirus ba ta shiga jihar ba. Ko ma ta shiga, to ana kokarin ganin an dakile ta daga barkewa.” Inji sanarwar.
Daga nan ya shawarci jama’a a bi dokar gwamnati kuma a bi ka’idojin da hukumomin lafiya suka gindaya.
A jihar Bayelsa kuma an hana motocin taksi daukar fiye da fasinjoji biyu a baya. Sannan kuma an umarci direbobin su dauki fasinja daya kawai a gaba.