Ministan ilimi Adamu Adamu ya bayyana cewa gwamnati za ta ciyo bashin Naira biliyan 45 daga asusun ‘Global Partnership for Education (GEP)’ domin rage yawan yaran dake gararamba a kasar nan.
Adamu ya ce gwamnati ta ciyo bashin Naira biliyan 220 daga Bankin duniya domin cin ma wannan buri a kasar nan.
Bincike ya nuna cewa akwai yara sama da miliyan 10 da basu makarantan boko a kasar nan.
Ministan ilimi ya fadi haka ne a taron kungiyar kasashen rainon Ingila ta shekarar 2020 da aka yi a Abuja.
Taken taron na bana shine samar da dawwamammiyar ci gaba a kasashen dake rainon Ingila sannan da tattauna hanyoyin da wadannan kasashe za su bi wajen samun ci gaba.
Adamu yace ma’aikatar ilimi ta tsaro shirin ilimantar da horas da mata matasa musamman masu shekaru 12 zuwa 20 domin rage yawan matan da basu da ilimin boko a kasar nan.
Ya ce shirin zai dauki tsawon shekaru biyu kuma shirin ya samu goyan bayan babbar bankin duniya.
Bayan haka kungiyar kasashen rainon Ingila ta tallafa wa mutane sama da 2000 a kasar nan tun bayan kafa kungiyar.
Duk shekara kungiyar kan ware isassun kudade domin tallafa wa ilimin bokon yara 12 zuwa 18.
Daga nan kuma ma’aikatar ilimi ta tsaro hanyoyin tallafa wa mutane 450 a Najeriya.
Karamin ministan ilimi Emeka Nwajiuba ya ce ma’aikatar ilimi ta tsara wasu shirye-shirye da za a rika koyar da yara a makarantu da suka hada da koyon raira wakoki, rawa, wasan kwaikwayo da sauran su domin karkato da hankulan su wajen gane karatu da wuri.
A karshe sarauniyar kasar Ingila Elizabeth ta jinjina hadin kan da kasashen dake karkashin wannan kungiyar ke da shi.
Sarauniya Elizabeth ta yi kira ga kasashen da su ci gaba da hada kansu dimin samun ci gaba a kasashen su.