Gwamnati ta rufe filin jiragen saman Aminu Kano, da wasu Uku, banda Abuja da Legas

0

Kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar cutar coronavirus ya sanarvda rufe wasu manyan filayen jiragen saman Najeriya guda uku.

Wannan doka zai fara aiki ne daga daren Juma’a.

Tashoshin da wannan doka ya shafa sun hada da tashar jirgin saman Aminu Kano dake Kano, da na Enugu da na Fatakwal.

Gwamnati ta ce tashoshin Legas da Abuja za su ci gaba da aiki, sai dai za a tsaurara matakan bincike da yin gwaji.

Kwamitin ta gargadi matafiya da su ba da hadin kai a flayen jiragen saman.

A Najeriya, akwai akalla mutane 12 da aka tabbatar sun kamu da cutar. Sannan mutum biyu da ya hada da wanda ya cara shigo wa Najeriya da cutar dan kasar Italiya, sun warke.

Gwamnatin Najeriya ta sanar da rufe makarantun kasar sannan ta yi kira ga mutane da su rika kauce wa shiga tarukka da cunkoson mutane.

Sannan kuma arika tsaftace muhalli.

Idan ba a manta ba, uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta bayyana cewa ‘yarta na nan a Killace a fadar gwamnati bayan ta dawo da kasar Birtaniya ranar Alhamis.

Aisha ta rubuta a shafinta ta Tiwita, sai dai bata bayyana ko wace ce daga cikin ‘ya’yan nata ba.

Tace sun bi umarnin kwamitin shugaban kasa na dakile yaduwar cutar, shine yasa a ka killace yarinyar bayan ta dawo daga kasar Birtaniya.

” Bayan haka na rufe ofishina na sati biyu saboda akwai wasu ma’aikata na da suka dawo daga kasar Birtaniya suma. Kowa yayi zai yi aiki daga gida.

Bayan haka ta yabawa gwamnonin Arewa Maso Yamma da suka rufe makarantu gaba daya zuwa wata mai zuwa.

” In Allah ya yarda za a ciwo karfin wannan cuta idan dukkan mu muka hada hannu, muka bi shawarar da ake bayar wa domin kada a kamu da cutar.

Sai dai kuma ‘yan Najeriya da dama da suka tofa albarkacin bakin su gane da wannan abu sun ce wata kila dalilin da ya sa kenan Najeriya taki rufe tashoshin Jiragen Saman ta sai yanzu.

Jami’ar John Hopkins dake kasar Amurka ta bayyana cewa mutane sama da 200,000 ne ke dauke da cutar coronavirus a fadin duniya.

A dalilin haka kasashen duniya da dama sun hana jiragen sama sauka da tashi a kasashen su, sun rufe iyakokin kasashen su na kasa sannan wasu sun kafa dokar hana walwala domin dakile yaduwar cutar.

Bisa ga rahoton, mutane 201,000 ne suka kamu da cutar sannan 8,000 sun mutu.

Rahoton ya kuma bayyana cewa kasar Chana da a nan ne cutar ta fara barkewa ta fara samun ragowar yaduwar cutar.

Duk da haka kasar ce ta fi kowacce kasa a duniya yawan mutanen da suka kamu da cutar da yawan wadanda suka mutu.

Zuwa yanzu mutane 82 suka warke daga cutar sannan 3,000 sun mutu.

Italiya ce kasar dake biye da Chana inda a kasar mutane 31,500 suka kamu da cutar, 2,500 sun mutu.

Ma’aikatan kiwon lafiya sun yi kira ga kasashen duniya da su karfafa matakan hana yaduwar cutar amma kuma wasu kasashen duniya na kukan rashin isassun kayan gwajin cutar.

Idan ba a mata a ranar Laraba ne ba kungiyar kiwon lafiya (WHO) ta sanar cewa mutane 600 ne ke dauke da cutar sanna 41 sun warke a kasashen Afrika.

WHO ta kuma sanar ranar Alhamis cewa a cikin awa 24 mutane 17 sun mutu sannan mutane 633 na dauke da cutar a Nahiyar Afrika.

Kwayoyin cutar Corona Virus na daga cikin kwayoyin cutar dake sa a kamu da mura wanda idan yayi tsanani akan yi fama da matsalar cutar dake hana numfashi yadda ya kamata da ake kira (Middle East Respiratory Syndrome (MERS-CoV), da kuma cutar tsanannin mura da kan toshe makogoro.

Alamun kamuwa da cutar sun hada da matsala a kafofin wucewar iska a makogoro wato numfashi, yawan zazzabi, tsananin tari, da ciwo a makogoro.

Idan abin yayi tsanani, ya kan kai ga shakar iska ma ya gagara, sannan a samu matsalar sanyin hakarkari wato ‘Nimoniya’, kuma idan har ya yi tsanani matuka kodar mutum kan daina aiki kwata-kwata.

Za a iya kaucewa kamuwa da wannan cuta ta hanyar, yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu, sannan a rika rufe hanci da baki idan za ayi atishawa kuma a rika wankewa da dafa nama sosai ya nuna tubus kafin a ci da kwai.

A rika nisanta ko kuma zama kusa da wanda ya nuna alamun rashin lafiya musamman irin wadanda a ka lissafa a sama sannan a gaggauta zuwa asibiti da neman magani idan ba a da lafiya.

Share.

game da Author